Rashin tsaro: Bidiyo ya bayyana yayin da Sheikh Gumi ya ziyarci mahaifar Sunday Igboho
- Shahararren malamin addinin Musulunci mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya jaddada bukatar hada kan Najeriya
- Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne lokacin da shi da tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, suka ziyarci Igboho a jihar Oyo
- Igboho ya kasance mahaifar mai fafutukar neman kasar yarbawa, Sunday Adeyemi wanda aka fi sani da Sunday Igboho
Igboho, Oyo - Sheikh Ahmad Gumi, malamin addinin Islama na jihar Kaduna, ya ziyarci garin Igboho da ke jihar Oyo, garin mai fafutukar kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.
Legit.ng ta rahoto cewa an ga Gumi a garin Igboho tare da tsohon babban jami'in hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.
An ga Gumi da Yusuf tsaye a gaban allon makarantar Muslim Grammar a Modeke-Igboho a wani faifan bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa.
Ya bayyana cewa bai ga abin da zai ba mutane damar tayar da hankali kan cewa a raba su da Najeriya ba.
Sheikh Gumi ya ce:
"A yau mun ziyarci wannan gari na Igboho, garin Musulmai ne kuma muna iya ganin wasu shanu suna kiwo a farfajiyar su.
"Wannan wuri ne da nake ganin ya kamata 'yan Najeriya su fahimci cewa muna bukatar zama tare. Domin ban ga wani abu a nan ba da zai ba mutane damar tayar da hankali cewa ya kamata a raba su da kasar mu abin kaunan mu."
Yusuf ya kara da cewa manyan mutane ne ke raba Najeriya ba talakawa ba, lura da cewa talaka daya ne.
Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria
A wani labarin, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani da su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.
Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.
Asali: Legit.ng