Ziyarar Da Sheikh Gumi Ya Kai Garin Igboho 'Neman Rigima' Ne, In Ji Basarekan Yarbawa, Gani Adams

Ziyarar Da Sheikh Gumi Ya Kai Garin Igboho 'Neman Rigima' Ne, In Ji Basarekan Yarbawa, Gani Adams

  • Aareonakakanfo na kasar Yaraba, Gani Adams da sauran masu ruwa da tsaki na kungiyoyin jami’an tsaron kudu maso yamma sun soki ziyarar da Sheikh Gumi ya kai garin su Igboho
  • A wani bidiyo wanda yayita yawo a kafafen sada zumuntar zamani ranar Talata, an ga malamin addinin musuluncin a garin Igboho tare da tsohon shugaban inshora na lafiya, Farfesa Usman Yusuf
  • Hakan yasa su ka yi zargin ziyarar da Gumi ya kai garin na nuna cewa yana da hannu dumu-dumu a farmakin da jami’an DSS suka kai gidan Igboho a kwanaki

Jihar Oyo - Aareonakakanfo na kasar Yarabawa, Gani Adams da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaron kudu maso yamma sun yi suka akan ziyarar da Sheikh Ahmad Gumi ya kai garin su Igboho.

Kara karanta wannan

Kungiyar Oyo ta gargadi sarakunan gargajiya, tana so a binciki ziyarar da Gumi ya kai jihar

Bisa ruwayar The Punch, Mai rajin kare hakkin yarabawa, Chief Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho asalin dan Igboho ne, hedkwatar karamar hukumar Oorelope da ke jihar Oyo.

Ziyarar Da Sheikh Gumi Ya Kai Garin Igboho 'Neman Rigima' Ne, In Ji Basarekan Yarbawa, Gani Adams
Gani Adams, Sheikh Ahmad Gumi da Sunday Igboho. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Bayyanar bidiyon Gumi a garin Igboho ya janyo cece-kuce.

Bidiyon wanda ya yi ta yawo a kafafen safa zumunta a ranar Talata, anga babban malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna a garin Igboho tare da tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa, Farfesa Usman Yusuf.

Bayan wani taro na gaggawa, jami’an kungiyar tsaron ta bayyana ziyarar malamin a matsayin abin ban takaici.

Shugabannin jami’an tsaron sun bayyana hakan a wata takarda wacce SSSG Gani Adams da sakataren sa, Alhaji Owolabi Amusat, suka sa hannu wacce suka yi wa take da ‘Rashin tsaro: Ku kiyayi kudu maso yamma, kungiyar jami’an tsaron kudu maso yamma ta ja kunnen ‘yan bindiga’.

Kara karanta wannan

Yan kabilar Igbo ke rike da tattalin arzikin Najeriya, saboda me zasu bar kasar: Shugaba Buhari

Sun caccaki ziyarar da Gumi ya kai garin Igboho, inda su ka ce ya je ne 'don ya yi isgili da kuma nuna raini ga kokarin masu rajin kare hakkin yarabawa'.

Sun yi zargin Sheikh Gumi yana da hannu a farmakin da DSS ta kai gidan Igboho

Sun ce alamu sun nuna cewa ziyarar Malamin zuwa garin Igboho yana nuna cewa:

“yana da hannu a farmakin da DSS ta kai wa gidan Igboho, kuma hakan yana nuna cewa ya fara mallake wani bangare na kasar yarabawa”.

A matsayin Gumi na dan Najeriya, yana da damar da zai ziyarci duk inda yake so a fadin Najeriya matsawar hakan ba zai kawo muzanci ga garin Igboho ba.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

“Wannan abin ban takaici ne kuma zai iya tayar da tarzoma. Duk wasu ra’ayoyin Gumi suna kaucewa daga yadda tunanin mutanen kasar nan suke. Ina ganin gara ya hakura da zuwa bangaren mu da kuma rura watar da bai san karshen ta ba,”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Bidiyo ya bayyana yayin da Sheikh Gumi ya ziyarci mahaifar Sunday Igboho

Masu ruwa da tsakin harkar tsaron sun ja kunnen duk wasu ‘yan bindiga da miyagun mutane da su kiyaye kudu maso yamma.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, takardar ta kara da, “Saboda haka ne jami’an tsaron yankin kudu maso yamma suka kara yawan ‘yan sanda a yankin da duk wasu jami’an tsaro don tabbatar da cewa wurin ya tsira.

Sheikh Gumi ya faɗawa Fulani yadda za su yi wa kansu gata a Nigeria

A wani labarin daban, Malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Dr Ahmad Gumi, ya yi kira ga fulani a su tabbatar sun yi rajista sun kuma karbi katin zabe gabanin babban zaben 2023 da ke tafe a kasar, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, samun katin zaben yana da muhimmanci domin hakan zai basu damar zaben shugabanni da za su yi jagoranci na gari sannan su kare musu hakkokinsu.

Kara karanta wannan

Yan fashi sun taremu a hanya, sun kwace takardun kotu hannunmu, Lauyoyin DSS ga Alkali

Gumi ya ce akwai bukatar Fulani su yi rajistan kamar sauran yan Nigeria, domin su zabi mutanen da za su kiyayye musu dabobinsu da dukiyoyinsu da rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164