Mata a Afghanistan sun yi dandazo don nuna goyon bayansu ga mulkin Taliban
- Yayin da duniya ke ganin Taliban za su wulakanta mata, sai ga mata a kasar sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan Taliban
- Wannan ya faru ne a ranar Asabar a bikin cika shekara 20 na kai hari kan cibiyar kasuwanci dake Amurka a 11/9
- Mata da dama sun fito rike da tutoci suna nuna goyon baya ga Talihan tare da yin kabbara ga kungiyar
Afghanistan - Daruruwan mata, sanye da burka, sun yi maci a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, dauke da alamun nuna goyon baya ga kungiyar Taliban, kamar yadda rahoton Al Arabiya ya fada a ranar Asabar 11 ga watan Satumba.
Mata da dama, wadanda suka lullube daga kai har zuwa kafa kuma suka lullube fuskokinsu, sun yi zanga-zanga a waje da cikin Jami'ar Ilimi ta Shaheed Rabbani, dauke da tutocin Taliban.
A baya-bayan nan kungiyar Taliban ta kafa dokar kebe jinsi a makarantu inda aka raba dalibai maza da mata da labule.
Matan masu zanga-zanga a kan titi sun gamu da mayakan Taliban dauke da bindigogi masu sarrafa kansu, kuma ba su bari masu wucewa da 'yan jarida su tattauna da matan ba, in ji rahoton New York Times.
Meye ya jawo zanga-zangar?
Zanga-zangar ta zo ne a bikin cika shekaru 20 da harin 9/11 kan cibiyar kasuwanci dake Amurka wanda ya haifar da "yakar ta'addanci" da mamayar Amurka a Afghanistan.
Bayyanar matan ya dawo da tunanin zamanin mulkin Taliban na 1996-2001, lokacin da aka hana mata barin gidajensu ba tare da rakiyar namiji ba, dole ne su lullube fuska, kuma ba a ba su damar yin aiki a yawancin ayyuka ba sai a fannin kiwon lafiya.
Tun bayan da Taliban ta kwace mulki a ranar 15 ga watan Agusta, ta bayyana sauyin ra'ayoyi daban-daban masu tsauri, tare da bayyana cewa za ta dama da mata a fannonin daban-daban na mulkin kasar.
Sai dai, masu fafutukar mata da tsoffin shugabannin siyasa na mata sun ce suna tsammanin za a dauke su a matsayin masu daraja ta biyu a cikin al'umma.
Kalli bidiyon zanga-zangar:
Amurka ta gama ficewa daga Afghanistan, jirgin karshe ya tashi ranar Litinin
A wani labarin, Hukumomin Amurka a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta sun sanar da cewa dukkan dakarunta sun fice daga kasar Afghanistan.
Jaridar Fox News ta ba da rahoton cewa jirgin C-117 na karshe dauke da membobin aiki na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman Kabul da misalin karfe 3:29 na yamma agogon Amurka.
Fadar White House ta ce a cikin awanni 24 daga safiyar Lahadi, 29 ga Agusta zuwa Litinin, Amurka ta kwashe mutane 1,200 daga Kabul, tare da jiragen soji 26 da jiragen hadin gwiwa guda biyu dauke da wadanda suka fice daga kasar Afghanistan.
Asali: Legit.ng