'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane huɗu da ƙoƙon kan ɗan adam
- Yan sanda a jihar Kogi sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da fashi da makami su huɗu
- Bayan kama su, an kuma kwato muggan makamai, bindigu, harsashi da ƙoƙon kan ɗan adam
- 'Yan sandan sun ce sun amsa aikata wasu laifukan kuma da zarar an kammala bincike za a kai su kotu
Jihar Kogi - Rundunar ƴan sanda na jihar Kogi ta ce ta kama wasu mutane hudu da ta ke zargin masu garkuwa ne da fashi da makami da ke adabar mazauna ƙaramar hukumar Bassa da kewaye, Daily Trust ta ruwaito.
DSP William Ayah, mai magana da yawun yan sandan jihar ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar, rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce an kwato makamai hannun waɗanda ake zargin da suka hada da pistol ƙirar gida, harsashi 7.62mm, bindigan G3 da ƙoƙon kan ɗan adam biyu.
Sanarwar ta ce:
"Bayan samun bayanan sirri cewa an gano masu garkuwa da yan fashi da ke adabar mutanen karamar hukumar Bassa da kewaye a wani gida da ke new Jerusalem Oguma a Bassa, jami'an yan sandan na Bassa karkashin jagorancin DPO sun kai samame."
"Sun yi dirar mikiya a gidan kuma suka kama wadanda aka zargi da suka hada da Guda Dangana, Dogo Chure, Dakuna Zhiya da Samson Nyizo duk yan ƙaramar hukumar Bassa."
Waɗanda ake zargin sun amsa laifin su
Sanarwar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata wasu laifuka a Bassa da kewaye kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Ta kara da cewa:
"Kwamishinan yan sanda, CP Idrisu Dauda Dabban, yayin da ya ke yabawa jami'ansa, ya bawa mutane da ƴan jihar Kogi cewa yan sandan da hadin gwiwa da sauran jami'an tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wurin tabbatar da tsaro."
Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa
A wai labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.
Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng