Abubuwa 6 da ya dace a sani a game da sabon Hukumar NCDC da Shugaban kasa ya nada
- Dr. Ifedayo Morayo Adetifa zai dare kujerar Darekta-Janar a hukumar NCDC
- Rahotanni sun bayyana cewa Dr. Adetifa ya yi karatu a Najeriya da Amsterdam
- Sabon Darektan ya kusa zama Farfesa a wata makarantar tsabta da ke Landan
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Dr. Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin Darekta-Janar na hukumar NCDC mai yaki da cututtuka a Najeriya.
Daily Trust ta tsakuro wasu abubuwa daga cikin tarihin sabon shugaban hukumar ta NCDC.
Ga wasu kadan daga cikin tarihin wannan kwararren likita wanda zai dare kujerar hukumar NCDC.
1. A ina yayi karatun digirin farko?
Ifedayo Morayo Adetifa ya samu digirin likitanci a jami’ar Ilorin da ke Kwara. Sannan ya samu hora a fannin duba kananan yara a asibitin koyon aiki na LUTH. A 2005 ne kungiyar likitoci ta Afrika ta yamma ta tabbatar da shi a matsayin kwararren likitan yara.
2. Ya yi digirgir da digir-digir a Amsterdam
Rahoton yace sabon shugaban na NCDC ya karanci ilmin karantar yadda cututtuka suke yadu wa al’umma a jami’ar Amsterdam, kasar Netherlands. A nan ya samu digirinsa na biyu da na uku.
3. Farfesa a makarantar Landan
Kafin ya samu wannan mukami a Najeriya, likitan ya kai matakin mataimakin Farfesa a cibiyar kula da cututtuka a makarantar tsabta da manyan cututtuka da ke Landan a kasar Ingila.
4. A wani bangare ya yi bincike da nazari?
A tsawon shekarun da ya yi yana karatu, Dr. Ifedayo Morayo Adetifa ya fi bada karfi wajen bincike a kan karfin magungunan cututtuka, dabarun rigakafi, da yadda cutar tarrin tibi ta ke yadu wa
5. Kungiyar MRC/DFID
A 2018 aka shigar da Morayo Adetifa cikin kungiyar MRC/DFID ta kwarrarun masu bincike a nahiyar Afrika. Sannan likitan ya na cikin kwamitin rigakafi da WHO ta kafa a kasar Kenya.
6. Aikin rigakafin cututtuka
Bayan haka, Dr Ifedayo Morayo Adetifa ya taka rawar gani a kwamitin kula da rigakafi a Kenya, da majalisar RITAG ta kungiyar WHO da kwamitin da aka ba nauyin rigakafin masassara a Afrika.
Kamar yadda kuka ji labari, Ifedayo Morayo Adetifa zai maye gurbin Dr. Chikwe Ihekweazu, wanda ya samu kujera a mai tsoka a kungiyar lafiya ta Duniya.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya aiko wa Chikwe Ihekweazu takarda yana sanar da shi zai rike kujerar shugaban sashen bada agajin gaggawa a kungiyar.
Asali: Legit.ng