Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba

Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba

  • Ministar tallafi da jin dadin jama'a ta bada shawarar sauya shugaban NAPTIP da sabuwa
  • Buhari ya amince da shawarar nadin Dr Fatima don maye gurbinsa
  • Garba Shehu yace Dr Fatima Waziri ta samu kwarewa daban-daban a rayuwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban hukumar hana safarar mutane watau NAPTIP, Sanata Basheer Garba Mohammed, daga kujerarsa a ranar Laraba, 8 ga Satumba, 2021.

Buhari ya sallami Basheer ne bayan kimanin watanni hudu da nadashi.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana jawabin da ya saki da yammacin nan cewa Buhari ya maye gurbin Sanata Bashir da Fatima Waziri-Azi.

Shehu ya saki jawabin a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, Buhari ya nada Fatima Waziri-Azi ne bisa shawarar da Ministar tallafi da walwala, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bashi.

Kara karanta wannan

Mataimakin Dirakta a ma'aikatar gwamnati ya hallaka kansa ranar da EFCC ta gayyaceshi

Garba Shehu yace Buhari ya amince da sabon nadin ne saboda kokari da jajircewan da Fatima Waziri-Azi ta sami a rayuwarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba
Shugaba Buhari ya sallami shugaban NAPTIP, Basheer Garba
Asali: Twitter

Kashi 55% na nade-naden da Buhari yayi yan kudancin Najeriya ya baiwa, Hadimin Shugaban kasa

Babban hadimin shugaban kasa kan lamuran jama'a, Ajuri Ngelale, yace wasu yan Najeriya kullum sun kiran shugaba Muhammadu Buhari da sunan mai nuna kabilanci.

Yayin hira da yan jarida a shirin 'Morning Show' na tashar AriseTV, hadimin shugaban kasan yace ko yaushe ana kokarin ganin Buhari na fifita Arewa.

Ngelale yace duk da soke-soken da ake yiwa Buhari, yana adalci wajen ganin kowa ya samu romin demokradiyya daidai wa daida.

Yace:

"Yayinda muka tattara dukkan nade-naden da yayi tun lokacin da ya hau mulki kawo yanzu, mun tarar da cewa kashi 55% na nade-naden gwamnatin nan yan kudu aka baiwa, mafi akasari yankin Kudu maso yamma (Yarbawa)."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng