Da Dumi-Dumi: Jami'an Amotekun Sun Ceto Matafiya 9 da Ɓarayi Suka Sace a Ondo
- Jami'an Amotekun na jihar Ondo, sun samu nasarar kuɓutar da matafiya 9 daga cikin 12 da yan bindiga suka sace a Ondo
- Rahotanni sun bayyana cewa matafiyan na kan hanyarsu ta zuwa Lagos daga Abuja, yayin da lamarin ya auku da su a hanyarAkoko-Idoani
- Kwamandan jami'an Amotekun, Chief Adetunji Adeleye, yace jami'ansa sun faɗa jeji domin ceto ragowar mutum uku dake hannun ɓarayin
Ondo - Jami'an tsaron jihar Ondo, Amotekun, sun ceto mutum 9 daga cikin matafiya 12 da aka sace a jihar, ranar Laraba da yamma a kan hanyar Akoko-Idoani.
Leadership ta ruwaito cewa yan bindiga sun yi awon gaba da wasu fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Lagos daga Abuja, a cikin wata motar Bas mai ɗaukar mutum 18.
Kwamandan jami'an Amotekun, Chief Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa jami'ansa sun samu nasarar ceto fasinjojin ne bayan samun bayanan sirri daga mazauna yankin.
Zamu kubutar da sauran matafiyan
Da yake zantawa da manema labarai, Adeleye, yace jami'ai sun tsunduma cikin jeji domin kuɓutar da sauran fasinjojin guda uku da suka rage.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kwamandan Amotekun ya bayyana cewa ba'a cafƙe kowa ba da ake zargin yana da hannu a sace mutanen.
A jawabinsa, Adeleye yace:
"Jami'an mu sun ɗauki mataki nan take bayan jin ƙarar harbi da kuma kiran waya da aka musu aka basu wasu bayanai."
"Sun isa wurin a lokacin da ya dace, kuma suka samu nasarar ceto mutum 9. Jami'an sun kai matafiyan ofishin Amotekun dake Isua, daga baya aka sake su bayan sun samu kulawar da ya dace."
"Mun kaiwa hukumar yan sanda motar bas ɗin da kuma direbanta, a halin yanzun jami'ai na cigaba da bincike domin kubutar da ragowar mutum uku da suka rage hannun ɓarayin."
Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara
A wani labarin kuma akwai matukar wahala jagorancin ma'aikatar noma, Nanono bayan Buhari ya sallame shi
Nanono ya faɗi haka ne a wurin taron mika harkokin ma'aikatar ga sabon minista, Dr Mohammad Mahmood Abubakar.
Yace komai yan Najeriya suka kwaso sai ace laifin ma'aikatar noma ne, amma duk da haka mun samu nasara.
Asali: Legit.ng