Na ga abubuwan da suka tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo

Na ga abubuwan da suka tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo

  • Bayan ziyarar da ya kai jihar Imo, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gamsuwa kan kokarin gwamna Hope Uzodinma a jihar
  • Shugaban wanda ke kaddamar da wani muhimmin aiki a jihar, ya yaba da halin gwamnatin jihar
  • Buhari ya lura cewa nasarorin da shugaban na jihar Imo ya samu duk da mawuyacin hali da ake ciki yakamata a yaba masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya ga abin da ya isa a jinjina wa namijin kokarin Gwamna Hope Uzodinma.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa Buhari ya yi wannan furuci ne a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, a lokacin da ya kai ziyara jihar Imo inda ya kaddamar da aiyukan da gwamnatin ta gudanar.

Na abun da ya tabbatar da mutuncin Uzodinma, cewar Buhari yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo
Buhari ya jinjina wa Hope Uzodinma yayin da ya kaddamar da ayyuka a Imo Hoto: Francis Nwaze
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya ce manyan ayyukan shugaban na jihar Imo ya birge shi duk da yanayin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

Buhari yace:

"Na ga abin da ya isa ya tabbatar da mutuncin Uzodinma wajen ganin cewa yana aiki tukuru don tabbatar da ganin cewa kun sami abubuwan da ake buƙata.
"Abun da yayi ya matukar burge ni saboda na fuskanci irin wannan matsalar a cibiyar."

Ya tabbatar wa mazauna Imo cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa jihar a cikin tanade -tanaden kundin tsarin mulkin.

Shugaban kasar ya kaddamar da ayyuka da suka hada da titin Ihiagwa zuwa Nekede, Fasahar Balloon wacce aka yi gada ta karkashin kasa ta bullo ta saman titin Chukwuma Nwoha, titin Naze/Nekede/Ihiagwa, Egbeda By-Pass.

Sauran ayyukan da ya kaddamar sun hada da sabbin gine-ginen zauren majalisa a cikin gidan Gwamnati da aka fi sani da Douglas House.

Ana kuma sa ran zai halarci wani taro tare da shugabanni kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Zan taimakawa jihar Imo wajen magance matsalar tsaro, Shugaba Buhari

A gefe guda, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, ya yi alkawarin taimakawa gwamnan jihar imo, Hope Uzodinma, wajen kawo cigaba a jiharsa ta hanyar samar da ayyuka.

Hakazalika Buhari ya bada tabbacin cewa zai yi amfani da ikonsa wajen taya gwamnan magance matsalar tsaro.

Buhari, wanda yayi magana yayin kaddamar da titin Egbeada-Onitsha a Owerri, yace ya gamsu gaskiya a ayyukan da gwamnan yayi, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel