'Yan fashin daji sun sheke dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a yankunan Kaduna

'Yan fashin daji sun sheke dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a yankunan Kaduna

  • ‘Yan bindiga sun hallaka sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 a wani farmaki da suka kai karamar hukumar Chikun
  • An samu rahotanni a kan yadda ‘yan bindigan suka yi ta harbe-harbe a kauyen yayin da jama’a suka yi ta gudun neman tsira
  • Ganau sun tabbatar da yadda suka yi asubancin kai hari Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar a ranar Laraba

Kaduna - ‘Yan bindiga sun yi ajalin wani sifetan ‘yan sanda sannan sun yi garkuwa da mutane 23 sakamakon wani hari da suka kai Unguwan Maje da Unguwan Laka da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

TheCable ta fahimci yadda ‘yan bindigan suka kai farmakin da safiyar ranar Laraba.

'Yan fashin daji sun sheke dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a yankunan Kaduna
'Yan fashin daji sun sheke dan sanda 1, sun iza keyar mutum 23 a yankunan Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An samu bayanai a kan yadda suka yi ta harbe-harbe ‘yan kauyen suna gudun neman tsira, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

Wani ganau ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Da farko sun fara kai farmaki Unguwan Maje ne, inda suka yi garkuwa da mutane 15 wanda yawancin su mata ne da yara.
“Daga baya suka nufi Unguwan Laka inda suka hallaka wani sifetan ‘yan sanda, Joshua Markus daga zuwan sa ziyarar ‘yan uwansa tun daga jihar Rivers.
“Yan bindigan sun yi garkuwa da mutane 7 ciki har da mata da diyar wanda suka hallaka.”

Wani soja mai murabus, wanda dan Unguwan Laka ne ya samu nasarar tserewa da iyalin sa dakyar. Sai dai sun babbaka motarsa da babur dinsa.

An ajiye gawar sifetan a asibitin Saint Gerald Catholic da ke cikin Kaduna.

Da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, Mohammed Jalige, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.

Amma ya yi alkawarin bincike a kai, kawo lokacin rubuta rahotan nan, ba a samu jin komai daga bakinsa ba.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun sace kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa daf da aurenta

Jihar Kaduna ta na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro da kuma garkuwa da mutane har da hallaka su kusan kullum.

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

A wani labari na daban, sabon ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya bayyana burinsa na yin aiki tare da duk ma’aikatansa don faranta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya rai.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Injiniya Aliyu ya sanar da manema labaran gidan gwamnati hakan bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce ya je fadar ne musamman don su tattauna da Buhari a kan yadda zai tafiyar da ayyukan sa inda yace, idanun ‘yan Najeriya yana kan ma’aikatar sa kuma za su bukaci ganin wani abu mai kyau da zai fito daga nan.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng