Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

  • Sabon ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu ya bayyana niyyar sa ta yin aiki tukuru don faranta wa shugaba Buhari da ko wanne dan Najeriya rai
  • Injiniya Aliyu ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labaran gidan gwamnati suka yi da shi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata
  • A cewar ministan, ya je fadar shugaban kasa ne musamman don su tattauna a kan yadda zai fara ayyukan sa a subuwar ma’aikatar inda ya ce idanun ‘yan Najeriya suna kan shi

Aso Villa, Abuja - Sabon ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya bayyana burinsa na yin aiki tare da duk ma’aikatansa don faranta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya rai.

Kara karanta wannan

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

Daily Trust ta ruwaito cewa, Injiniya Aliyu ya sanar da manema labaran gidan gwamnati hakan bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata.

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki
Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ministan ya ce ya je fadar ne musamman don su tattauna da Buhari a kan yadda zai tafiyar da ayyukan sa inda yace, idanun ‘yan Najeriya yana kan ma’aikatar sa kuma za su bukaci ganin wani abu mai kyau da zai fito daga nan.

Ya kara da bayyana niyyarsa ta aiki tare da duk wasu masu ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki don kara wa rayuwar kowa armashi, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar sa:

“Kamar yadda ku ka sani, a makon da ya gabata aka daura ni a mukamin nan. An daura ni a matsayin ministan ma’aikatar wutar lantarki a lokacin na kadaice kai na saboda tafiyar da na yi kasar ketare.

Kara karanta wannan

Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure

"Ban iso gida ba sai ranar Litinin. Na kuma koma kan aikin da aka daura ni a matsayin ministan wutar lantarki. Na zo ne don mu tattauna da shugaba Buhari saboda jiya na fara zama da ma’aikatan ma’aikatar.
“Don haka, ina so in kara fadada ma’aikatar in hada ta wuri guda da Gencos, TCN da DISCOs.
“Bayan na kammala tattaunawa da masu hannayen jari a ma’aikatar da sauran ma’aikatan ta, shi ne nace ya kamata mu zauna da ku. Ina bukatar addu’o’i da goyon baya.”
“Sakamakon yadda shugaban kasa ya yarda da ni har ya daura ni a mukamin nan, zan yi iyakar kokari na na ganin na faranta wa kowa rai InshaAllah.”

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

A wani labari na daban, zauren dattawan arewa, NEF, a ranar Litinin ya ce ba ya sukar matakan tsaron kasa da wasu gwamnonin jihohin arewa maso yamma suka dauka da jihar Niger domin dakile miyagun hare-haren 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Rashin kwazo: An gano sahihan dalilan da suka sa Buhari ya sallami Nanono da Mamman

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnonin sun dakatar da kasuwannin da ake ci duk mako tare da hana siyar da fetur a jarkoki da kuma sauran hanyoyin dakile matsalolin tsaro a jihar.

A wata takarda ta ranar Lahadi, daraktan yada labarai na kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce dukkan matakan da aka dauka za su iya sa miyagun su sake balle ta'addanci a yankunan da babu tsaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng