Katsina: ‘Yan bindiga sun sace kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa ana daf da aurenta

Katsina: ‘Yan bindiga sun sace kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa ana daf da aurenta

  • ‘Yan bindiga sun sace wata Budurwa da ke shirin aure a wani Kauyen Katsina
  • Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya tabbatar da cewa wanda aka dauke kanwarsa ce
  • Miyagun ‘Yan bindigan sun shiga har gidan Mai Unguwa ne suka yi gaba da su

Katsina - Wani rahoto maras dadi yana cewa an dauke kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Katsina, Honarabul Shehu Dalhatu Tafoki.

Jaridar Daily Trust da ta kawo wannan rahoton a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, 2021, tace ana zargin ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Asma’u Dalhatu.

Kamar yadda jaridar ta wallafa, ‘dan majalisar, Shehu Dalhatu Tafoki, ya bayyana cewa an dauke ‘yaruwar ta sa a sa'ilin da ake shirye-shiryen yi mata aure.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Mai sarauta, sun dauke mutane a jihar Shugaban kasa

Ya abin ya faru?

‘Yan bindiga sun shiga kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskari, suka dauke budurwar da wata ‘yaruwarta wanda Allah ya yi wa gyadar-doguwa.

“Eh, da gaske ne, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kanwata, Asma’u Dalhatu a safiyar ranar Lahadi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Sun dura garin da kimanin karfe 1:00 na dare, suka zarce kai-tsaye zuwa gidan Mai gari, wanda nan ne gidan gadonmu.”
'Dan Majalisar Faskari
Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki a zaben APC Hoto: @dalshehu /Facebook
Asali: Facebook

Daya daga cikin 'yan matan ta tsere

“Sun yi garkuwa da wasu biyu daga cikin ‘yanuwanmu.”
"A hanyar shiga jeji, suka ci karo da wasu ‘yan sa-kai, aka yi barin wuta. A sanadiyyar haka ne daya daga cikin ‘yan matan ta tsere, ta dawo gida.”
“Sai dai dayar ba ta yi dace ba, ba ta iya kubuta ba, saboda haka suka tafi da ita.”

Zuwa yanzu, Shehu Tafoki yace ‘yan bindigan ba su tuntube su domin su nemi a biya kudin fansa ba. Wannan Baiwar Allah tana shirin zuwa gidanta na aure.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi

An ji cewa an samu wasu miyagun da suka sheka da wani Basarake barzahu a Kauyen Masaka da ke Gundawa, karamar hukumar Kankara, jihar Katsina.

Mutanen Kauyen na Masaku suna makokin mutuwar Mai Unguwarsu da aka hallaka kwanaki kadan bayan gwamna ya ba mutane shawarar su kare kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel