'Yan bindiga sun sheke rayuka 300, mutum 3,000 sun rasa muhalli a Niger ta gabas, Sanata

'Yan bindiga sun sheke rayuka 300, mutum 3,000 sun rasa muhalli a Niger ta gabas, Sanata

  • Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta gabas, Mohammed Sani-Musa, ya bayyana yadda ‘yan bindiga suka hallaka fiye da mutane 300
  • A ranar Talata, ya bayyana yadda suka janyo a kalla mutane 3000 suka rasa gidajen su a mazabar sa cikin watanni kadan da suka gabata
  • Ya bayyana hakan ne a wata takarda a Minna, inda ya kwatanta ayyukan ‘yan bindigan a matsayin mugunta da zalinci

Niger - Sanata mai wakiltar Neja ta arewa a majalisar tarayya, Mohammed Sani-Musa, a ranar Talata ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun hallaka fiye da rayuka 300 sannan sun hana fiye da mutane 3000 zama a gidajensu a cikin mazabar sa cikin watanni kadan da suka gabata.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda da Sani-Musa ya saki a ranar Talata a Minna ta jihar Neja, ya kwatanta ayyukan ‘yan bindigan a matsayin zalunci da mugunta ga dan Adam.

Kara karanta wannan

Ba mu da hannu cikin kashe-kashen matafiya a Jos, Matasan Irigwe sun magantu

'Yan bindiga sun sheke rayuka 300, mutum 3,000 sun rasa muhalli a Niger ta gabas, Sanata
'Yan bindiga sun sheke rayuka 300, mutum 3,000 sun rasa muhalli a Niger ta gabas, Sanata. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar sa:

“A cikin watanni biyu da suka gabata, a kalla mutane 3000 ne suka rasa gidajensu suka koma zama a sansanin ‘yan gudun hijira ,sannan sun yi asarar dukiyoyin su masu yawan gaske ta hanyar kwace ko kuma a lalata su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abin akwai tashin hankali kuma a haka suka kara afkawa garuruwan da ke karamar hukumar Shiroro ta mazabar a makon da ya gabata inda suka yi wa mutane 20 yankan rago.
“Sun hallaka ‘yan kauyen nan tamkar tumaki, abu ne da bai kamata a cigaba da amincewa da shi ba. Don haka dole ne mu tashi tsaye mu yi iyakar kokarin ganin an kamo su an yanke musu hukunci.

Sanatan ya yi kira a kan kawo karshen ta’addanci a garuruwa inda yace ya kamata gwamnati ta mike tsaye ta tsare rayukan jama’an karamar hukumar Shiroro da sauran bangarorin mazabar Neja ta gabas, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Mai sarauta, sun dauke mutane a jihar Shugaban kasa

“Yanzu mutanen mu sun dena zuwa noma gonakin su saboda ta’addanci,” a cewar sa.

Ya kuma roki gwamnatin tarayya ta kawo tsaro a bangaren Bass, Magami da garin Kukokki inda da aka turo jami’an tsaro amma kwanaki aka karbe su. Hakazalika, akwai bukatar sansanin soji a tsakanin karamar hukumar Shiroro da jihar Kaduna.

Babu shakka Buhari da 'yan Najeriya za su yi farin ciki da mu, Sabon Ministan lantarki

A wani labari na daban, sabon ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya bayyana burinsa na yin aiki tare da duk ma’aikatansa don faranta wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘yan Najeriya rai.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Injiniya Aliyu ya sanar da manema labaran gidan gwamnati hakan bayan kammala taro da shugaba Buhari a fadar sa da ke Abuja a ranar Talata.

Ministan ya ce ya je fadar ne musamman don su tattauna da Buhari a kan yadda zai tafiyar da ayyukan sa inda yace, idanun ‘yan Najeriya yana kan ma’aikatar sa kuma za su bukaci ganin wani abu mai kyau da zai fito daga nan.

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Asali: Legit.ng

Online view pixel