Ba mu da hannu cikin kashe-kashen matafiya a Jos, Matasan Irigwe sun magantu
- Kungiyar cigaban Irigwe, wata kungiyar kabila a Filato, ta musanta zargin mutanen ta ne suke da alhakin hallaka mutane 22 na titin Rukuba
- A ranar Litinin, shugaban kungiyar, Robert Dodo a wani taro a Abuja ya musanta mabiyansa ne suke da alhakin hallaka jama’a a ranar 14 ga watan Augusta
- A cewar Dodo, mabiyan sa suna cikin mutanen da suke jimami a kan rasa rayukan da aka yi sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai wa jama’a
Jos - Kungiyar cigaban Irigwe, wata kabila ta jihar Filato a ranar Litinin ta musanta zargin mutanenta da hallaka rayuka 22 na matafiya a tititin Rukuba da ke Jos a ranar 14 ga watan Augusta.
Shugaban kungiyar, Robert Dodo ya musanta zargin a wani taro da suka yi a Abuja. A cewar Dodo, mutanen sa suna cikin masu alhinin faruwar lamarin kuma suna cikin wadanda suka birne jama’an bayan ‘yan bindigan sun tafka aika-aikar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a cewar sa sai da mutanen yankin suka nemi izinin ‘yan sandan Jos wadanda suka samar da tsaro yayin birniyar.
Ya kara da cewa, ‘yan sandan sun bai wa masu makokin shawarar kada su bi ta titin Rukuba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A matsayinmu na mutane masu bin doka, mutanen Irigwe sun yi amfani da wani hanyar daban don su isa Miago.
“Ba mu da wata alaka da matafiyan da aka hallaka,” a cewar sa.
Dodo ya kara da musanta zargin da ake yi wa matasan Irigwe a kan harin da aka kai titin Rukuba, inda yace kazafi ne da makirci.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa zargin mutanen Irigwe sun sanya hannu a takardar yarjejeniyar zaman lafiya da makiyaya ba gaskiya ba ne, Daily Nigerian ta wallafa.
A cewar sa mutanen Irigwe ba su da matsala kuma suna da son zaman lafiya kuma suna kokarin ganin sun taya gwamnatin jihar ganin an kawo karshen tarzomar da ke jihar.
Zamfara: Dalibi mai shekaru 13 ya sanar da yadda ya kubuta daga miyagu duk da harbinsa da aka yi
A wani labari na daban, Samaila Dahiru, dalibin GDSS Kaya, ya bayyana yadda ‘yan bindigan da suka yi yunkurin halaka malaminsa suka harbe shi amma kuma ya tsira.
Dahiru, mai shekaru 13 ya samu rauni a cinyarsa yayim satar dalibai 73 daga makarantar wacce ta ke karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, TheCable ta wallafa.
Yayin tattaunawa da TheCable a ranar Asabar bayan an sallame shi daga asibiti, Dahiru ya ce sauran dalibai sun dauke shi a kafadun su yayin tafiya cikin daji.
Asali: Legit.ng