Dalilinmu na son a rage yawan Masallatai a Kano – Majalisar malaman jihar

Dalilinmu na son a rage yawan Masallatai a Kano – Majalisar malaman jihar

  • Majalisar malaman Kano ta yi tsokaci a kan dalilinta na neman a rage yawan Masallatai a jihar
  • A cewarta ta yi haka ne domin guje ma rarraba kai da zukatan al'umma
  • Majalisar ta kuma yi Allah wadai da malaman da ke kaskantar da kansu ta hanyar bin son ran 'yan siyasa

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar bayan kammala wani gagarumin taro da ta gudanar na kwanaki biyu a karshen makon da ya gabata jihar.

Ta ce ta yanke wasu shawarwari a taron ciki harda rage yawan bude masallatai barkatai, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Dalilinmu na son a rage yawan Masallatai a Kano – Majalisar malaman jihar
Majalisar malaman Kano ta ce a rage buɗe masallatai barkatai domin guje wa rarraba kai da zukatan al'umma Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Har ila yau majalisar ta yi kira ga malamai da limamai a kan su dinga raya masallatai da karatuttuka da lakcoci baya ga tsayar da sallah a cikinsu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara

Wani bangare na sanarwar ta ce:

"A rage buɗe masallatai barkatai domin guje wa rarraba kai da zukatan al'umma."

Majalisar Malaman ta kuma jadadda cewa taronta ya mayar da hankali sosai kan gudunmawar da malamai da limamai ke bayarwa wajen samar da tarbiya da inganta zaman lafiya da dora al'amura bisa tushen shari'ar Musulunci.

Sanarwar ta kuma nuna cewa mahalarta taron sun yi Alla-wadai da yadda wasu malamai suke zubar da martabarsu ta hanyar zama ‘yan abi yarima a sha kidan ‘yan siyasa.

Malaman jihar sun kuma sun kuma bayyana cewa akwai wasu bara-gurbin malamai da ke haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin majalisar malamai domin cimma burinsu na kashin kansu.

Ta kuma bukaci malamai da su zamo masu yin nasiha ga masu rike da madafun iko a dukkan matakai domin su sauke nauyin da ya rataya wuyansu.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

Daga karshe majalisar ta kuma jaddada cewa tana gudanar da ayyukanta ne bisa tsarin doka da aka yi mata rijista, don haka ta ja hankalin mambobinta cewa "babu wanda zai yi mata karfa-karfa ya sa ta yi abin da ya saɓa wa doka da ka'idoji da sharuɗɗanta."

Kotu ta bada umurnin a duba lafiyar kwakwalwa da kunnen Sheikh Abduljabbar

A wani labarin, kotun Shari'ar Musulunci dake shari'a kan kara da gwamnatin jihar Kano ta shigar da Sheik AbdulJabbar Kabara ya bada umurnin aje a duba lafiyar kwakwalwar Malamin.

Kotun dake zaune a Kofar Kudu ta bada wannan umurni ne a zaman da aka yi ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba 2021, rahoton BBC.

A cewar kotun, akwai bukatar gwada kwakwalwa da kunnuwan Malam Abduljabbar a asibitin Dawanau da na Murtala saboda rashin maganar da yayi lokacin da aka karanto masa tuhume-tuhume 4 da ake masa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

Asali: Legit.ng

Online view pixel