'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara

'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara

  • Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta yi ram da kwararren barawon motoci a Zamfara
  • Jami'ai sun kama Badawi Abdullahi Ahmed bayan bibiyarsa da suka yi tun daga Abuja kan wata sata da ya tafka
  • An yi ram da matashin mai shekaru 38 a Talatan Mafara dauke da makulli mai iya bude kowacce irin mota da kayan kanikanci

Zamfara - Badawi Abdullahi Ahmed matashi ne mai shekaru 38 wanda ake zargi da zama gagarumin barawon motoci a Abuja kuma rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya suka yi ram da shi a Zamfara.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami'an 'yan sanda daga Maitama suka bibiye shi har zuwa Talata Mafara da ke jihar Zamfara inda suka kama shi tare da abun hawan da ya sata.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke dan bautar kasa da ke safarar alawa mai bugarwa daga UK

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, Daniel Ndirpaya, ya ce Abullahi kwarrare ne wurin satar motoci a ma'adanar su.

'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara
Kwararren barawon motoci, Badawi Abdullahi Ahmed da aka damke a Zamfara. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Satar motar da yayi a cikin kwanakin nan ne yasa aka cafke shi. Wanda ake zargin ya saci wata mota kirar Toyota Corolla mai kalar bula mai lambar rijista FKJ 625 DV a titin Aguiyi Ironsi da ke Maitama a Abuja, lamarin da yasa jami'ai suka fara bibiyarsa.

Bayan damke shi da aka yi, jami'an sun kwace makulli mai bude kowacce irin mota daga hannun wanda ake zargi tare da wata jaka mai dauke da kayan kanikanci.

Za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan an kammala bincike kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Kwamishinan 'yan sandan babban birnin tarayya, Babaji Sunday, ya shawarci jama'a da su kara wa ababen hawansu tsaro domin gujewa miyagu ko bata-gari.

Zamfara: Dalibi mai shekaru 13 ya sanar da yadda ya kubuta daga miyagu duk da harbinsa da aka yi

A wani labari na daban, Samaila Dahiru, dalibin GDSS Kaya, ya bayyana yadda ‘yan bindigan da suka yi yunkurin halaka malaminsa suka harbe shi amma kuma ya tsira.

Dahiru, mai shekaru 13 ya samu rauni a cinyarsa yayim satar dalibai 73 daga makarantar wacce ta ke karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, TheCable ta wallafa.

Yayin tattaunawa da TheCable a ranar Asabar bayan an sallame shi daga asibiti, Dahiru ya ce sauran dalibai sun dauke shi a kafadun su yayin tafiya cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng