Abun Mamaki: Matar Shugaban Ƙasa Ta Fice Daga Fadar Gwamnati, Ta Koma Koyarwa a Kwaleji

Abun Mamaki: Matar Shugaban Ƙasa Ta Fice Daga Fadar Gwamnati, Ta Koma Koyarwa a Kwaleji

  • Matar shugaban Amurka ta fice daga fadar White House, inda ta rungumi sana'arta ta koyarwa a makaranta
  • Jill Biden, malamar koyar da rubutu ce tun mijinta Joe Biden, yana mataimakin shugaban ƙasa a zamanin mulkin Obama
  • Jill ta zama mace ta farko, tana lamba ɗaya a Amurka sannan tana sana'arta ta koyarwa

United State - Mace lamba ɗaya a ƙasar Amurka, Jill Biden, ta fice daga fadar shugaban ƙasa 'White House' domin ta maida hankali kan aikinta na koyarwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Jill tana koyar da rubutu a kwalejin Northern Virginia, inda ta zauna a matsayin cikakkiyar malama lokacin da take matar mataimakin shugaban ƙasa ƙarƙashin mulkin Obama.

Rahoto ya nuna cewa Jill ta koyar a kwalejin tsakanin 2008 zuwa 2016, lokacin mijinta Joe Biden, yana mataimakin shugaban ƙasa, Obama.

Kara karanta wannan

Mijina Ya Haukace, Baya Jimawa a Wurin Kwanciyar Aure, Wata Mata Ta Nemi Kotun Musulunci Ta Raba Aurensu

Matar shugaban Amurka, Jill Biden
Abun Mamaki: Matar Shugaban Ƙasa Ta Fice Daga Fadar Gwamnati, Ta Koma Koyarwa a Kwaleji Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matar shugaban kasan tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Koyarwa ba wai kawai aikin da nake yi bane, koyarwa shi ke ni."

Tarihin aikin ta na koyarwa

Tarihi ya nuna cewa Jill ta fara koyarwa ne a babbar makarantar St. Mark dake Wilmington kuma ta samu digirinta na uku a jami'ar Delaware.

A wani jawabi da Farfesa a bangaren sadarwa, Tammy Vigil, na jami'ar Boston, ya yi kan lamarin yace matar shugaban ƙasa mai ci kuma tana wani aiki "Babban lamari ne."

Farfesa Vigil, shine ya rubuta littafi kan matan shugabannin ƙasar Amurka biyu, Michelle Obama da kuma Melania Trump.

Lamarin sabon abu ne domin ba'a san matan shugaban ƙasa da fita su yi wani aiki a wajen fadar shugaban ƙasa ta white house ba.

Matan shugabannin Amurka basu irin haka

Matar tsohon shugaba, Laura Bush, ita ma malamar makaranta ce amma ta daina aiki lokacin da aka zaɓi mijinta, George Bush, a matsayin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

Bugu da kari Hillary Clinton da Michelle Obama, duk sun bar aikinsu yayin da mazajensu suka karbi jagorancin Amurka.

Dailytrust ta ruwaito cewa a matsayinta na mace lamba ɗaya, ita ce ta farko da ta fara haɗa aikinta da kuma ayyukan matar shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Mijina rikakken ɗan neman mata ne, ya kwanta da kawayena da kanwata, wata mata ta nemi kotu ta rabasu

Wani maigida ya shigar da matarsa ƙara kotu bisa zarginta da cin amanarsa a jihar Lagos.

Sai dai lamarin baiwa matar daɗi ba, inda tace dama can ita ke ciyar da shi, kuma ya kware wajen neman mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel