Mijina Rikakken Dan Neman Mata Ne, Ya Kwanta da Kawayena da Kanwata, Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Rabasu

Mijina Rikakken Dan Neman Mata Ne, Ya Kwanta da Kawayena da Kanwata, Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Rabasu

  • Wani maigida ya shigar da matarsa ƙara kotu bisa zarginta da cin amanarsa a jihar Lagos
  • Sai dai lamarin baiwa matar daɗi ba, inda tace dama can ita ke ciyar da shi, kuma ya kware wajen neman mata
  • Matar ta roki alkalin kotun ya amince da bukatar mijinta ya raba auren su, wanda ya shekara 33 suna tare

Lagos - Wata mata mai suna, Chima Udemi, ta shaidawa kotun yanki cewa mijinta, Tobechukwu, rikakken ɗan neman mata ne da ya taba kwanciya da yar uwarta, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Udemi ta bayyana haka yayin da take magana kan ƙarar da mijinta ya shigar da ita kotu bisa zargin tana cin amanarsa.

Miji da Mata na neman a raba aurensu a Kotu
Mijina Rikakken Dan Neman Mata Ne, Ya Kwanta da Kawayena da Kanwata, Wata Mata Ta Nemi Kotu Ta Rabasu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Udemi tace:

"Tobechukwu ya jima yana neman mata, ya taba kwanciya da ƙanwata da kuma wasu ƙawaye na."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai lokacin da ya guje ni da ƴaƴan mu guda bakwai, ya koma wurin wata budurwarsa da suke baɗala tare."
"Miji ne da kwata-kwata baya sauke nauyin dake kansa a matsayin shi na Uba. Ya bar mun komai, da gumi na nake ciyar da ƴaƴan mu."

Komai ni nake wa mijina

Udemi ta kara da cewa mijinta a gidanta yake zaune, ta ciyar da shi, ta shayar da shi, amma daga karshe ya matsawa rayuwarta.

Matar ta roki kotu matukar mijin ya matsa dole sai an raba auren su,to ya shirya fice mata daga gida.

Matar mai 'ya'ya bakwai kuma yar kimanin shekara 55 ta bukaci kotu ta amince da bukatar mijin ta na raba auren su.

Meyasa Tobechukwu ya shigar da ƙarar matarsa?

Wanda ya shigar da ƙara, Tobechukwu, ya bukaci alkalin kotun ya raba auren wanda suka shafe shekara 33 tare bisa zargin matarsa da cin amanarsa.

Yace:

"Matata tana wata mu'amala a bayan ido na da wani mutumi ɗan ƙauyen su. Ta taba yin tafiyarta tabarni da ƴaƴan mu na tsawon shekara 10."

"Ta bar gidan auren ta na tsawon shekara 10 ba tare da munsan inda taje ba, a shekarar 2020 ta dawo."

Bayan sauraron kowane ɓangare, Mai shari'a Adeniyi Koledoye, ya roki ma'auratan sun sanya wa zuciyoyinsu ruwan sanyi.

Koledoye ya sanar da ɗage sauraron karar sai zuwa 21 ga watan Satumba, 2021.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa minsitan sadarwa, Pantami, ya bayyana dalilin da yasa FG ta datse sabis ɗin jihar Zamfara.

Pantami yace ba ma'aikatarsa ce ta kirkiri katse layukan sadarwa ta hanyar dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a jihar ba.

Ministan yace hukumomin tsaro ne suka bukaci a katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara domin zai taimaka wajen magance ayyukan yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel