Babban Dalilin da Yasa Muka Katse Hanyoyin Sadarwa a Jihar Zamfara, Sheikh Pantami
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa hukumomin tsaro ne suka bukaci a katse hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara
- Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, shine ya faɗi haka jim kaɗan bayan taron FEC a Abuja
- Yace gwamnati ba ta da wani zaɓi, domin a shirye take ta yi duk abinda ya dace don kawo zaman lafiya a faɗin kasa
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana babban dalilin da yasa ta dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a jihar Zamfara, kamar yadda This Day ta ruwaito.
Gwamnatin tace ta katse hanyoyin sadarwa a jihar bisa yawaitar ayyukan yan Bindiga ne saboda hukumomin tsaro sun buƙaci hakan.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dakta Isa Pantami, shine ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron majalisar zartarwa (FEC) ranar Laraba a Abuja.
Ba hakanan muka ɗauki matakin ba
Pantami yace ba ma'aikatarsa ce ta kirkiri katse layukan sadarwa ta hanyar dakatar da ayyukan kamfanonin sadarwa a jihar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sheikh Pantami ya ƙara da cewa lokacin da hukumomin tsaro suka gabatar da bukatarsu a matsayin hanyar dakile ayyukan yan bindiga, gwamnatin tarayya ba ta musa musu ba.
Pantami yace:
"Ba wai hakanan muka ɗauki wannan matakin ba, hukumomin tsaro ne suka bukaci hakan domin zai taimaka wurin dakile ayyukan yan bindiga."
"Lokacin da suka gabatar da bukatar haka bamu da wani zaɓi, gwamnati a shirye take ta hakura da abinda take samu a ɓangaren domin samun zaman lafiya"
FG ta yi namijin kokari
Malam Pantami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a shirye take ta sadaukar da duk abinda take samu daga ɓangaren kamfanonin sadarwa domin samun tsaro a ƙasa
Ministan ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su fahimci matakan da aka ɗauka kuma su bada goyon bayan su ga jami'an tsaro wajen kawo ƙarshen lamarin.
A wani labarin kuma Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Bangaren Ilimi
Shugaba Buhari ya amince da sake maida wasu shugabanni a wasu hukumomi dake ma'aikatar Ilimi, kamar yadda punch ta ruwaito.
Hakanan kuma Shugaban ya yi wasu sabbin naɗe-naɗe a wasu hukumomin ilimi masu muhimmaci na kasa.
Asali: Legit.ng