Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci a Bangaren Ilimi
- Shugaba Buhari ya amince da sake maida wasu shugabanni a wasu hukumomi dake ma'aikatar Ilimi
- Hakanan kuma Shugaban ya yi wasu sabbin naɗe-naɗe a wasu hukumomin ilimi masu muhimmaci na kasa
- Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar ilimi, Mr Bem Goong, ya fitar
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin wasu sabbin shugabannin hukumomi dake karkashin ma'aikatar ilimi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar ilimi ta ƙasa, Mr Bem Goong, shine ya sanar da sabbin naɗe-naɗen a wani jawabi da ya fitar.
Goong yace shugaban ƙasa Buhari ya amince da sake naɗa shugaban hukumar rijistar malamai (TRCN), Farfesa Josiah Ajiboye, karo na biyu kuma zango na ƙarshe da zai shafe shekara 5.
Hakanan Buhari ya amince da sake naɗa Farfesa Bashir Usman, a matsayin shugaban hukumar wayar da kan fulani ta ƙasa, a karo na biyu kuma zango na karshe da zai shafe shekara 5, kamar yadda this day ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane sabbin naɗe-naɗe Buhari ya yi?
Goong ya bayyana sabbin naɗe-naɗen da Buhari ya amince da su, waɗanda suka haɗa da shugaban hukumar bada ilimin matasa, Farfesa Akpama Ibar.
Sai kuma shugaban ɗakin bincike na ƙasa, Farfesa Chinwe Anunobi, da kuma shugaban manyan makarantun horar da malamai (NTI), Farfesa Musa Maitafsir.
A jawabinsa Boong yace:
"Baki ɗaya sabbin naɗe-naɗen uku zasu fara aiki daga ranar 2 ga watan Satumba kuma kowannen su shine zangon farko da zasu shafe shekaru 5."
Buhari ya yi muhimman naɗi a baya
A ranar 20 ga watan Agusta, Buhari ya amince da sake naɗa Farfesa Ishaq Oloyede, a matsayin shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB).
Hakanan Buhari ya sake naɗa shugaban hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC), Farfesa Adamu Rasheed, zango na biyu da zai shafe shekara 5.
A wani labarin kuma Yan Kasuwa Sun Yi Fatali da Umarnin Gwamnatin Kaduna, Sun Koma Harkokinsu Kamar da a Kawo
Yan kasuwar Kawo dake jihar Kaduna sun yi watsi da umarnin gwamnatin Kaduna na dakatar da cin kasuwar mako-mako.
Rahoto ya nuna cewa masu siye da masu siyarwa sun koma kasuwar ta Kawo jiya Talata ba tare da tunanin komai ba.
Asali: Legit.ng