'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto

'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto

  • Yan bindigan da sojoji suka fatattaka daga Zamfara sun kai hari a jihar Sokoto
  • Wani mazaunin garin Sokoton ya ce yan bindigan sun sace a kalla mutane 20
  • Kwamishinan tsaro na jihar Sokoto ya tabbatar da cewa yan bindigan Zamfaran suna shigowa Sokoto

Jihar Sokoto - 'Yan bindigan da ake zargin sun tsere ne daga daga yankunan Bakura - Talata Mafara na jihar Zamfara, a ranar Talata, sun kai hari ƙaramar hukumar Dange Shuni a Sokoto sun sace a ƙalla mutum 20, Premium Times ta ruwaito.

A halin yanzu dai rundunar sojojin Nigeria da wasu hukumomin tsaro suna aikin ragargazar ƴan bindiga a dazukan Zamfara.

'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto
Taswirar Jihar Sokoto: Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Saboda aikin da sojojin ke yi an datse hanyoyin sadarwa na salula da kuma kasuwannin sayar da dabbobi da dakatar da sayar da fetur a jarka.

Jihohi irin su Sokoto, Katsina da Niger suma sun ɗauki matakai masu kama da irin na Zamfara.

Mazauna Ƙaramar hukumar Dange sun shaidawa BBC Hausa ƴan bindiga na kwararowa yankinsu a baya-bayan nan.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Garba Moyi ya tabbatar da lamarin amma ya ce gwamnatin tana ɗaukan matakan da suka kamata.

Ya ce ƴan bindiga daga Zamfara na shigowa Sokoto amma ba garkuwa da mutane suka yi ba kamar yadda aka yaɗawa sai dai hanyar tserewa suka nema.

Mr Moyi ya tabbatar cewa wasu lokutan ƴan bindigan na kai wa mazauna garin hari don tsorata su ko satar abinci a yayin da suke tserewa.

Wani mazaunin garin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce:

"Ko jiya Talata ƴan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun kai hari wani ƙauye mai suna Fajanbi sun sace mutum tara.

"Wani mutumin da aka sace daga wani ƙauye amma ya tsere ya faɗa mana cewa wadanda ƴan bindiga suka sace sun ɗara 20."

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

A wani labarin daban, kun ji cewa kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel