‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin Shugaban karamar hukuma a jihar Bayelsa
- Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Cif Gbalipre Turner, mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa, Hon. Ebinyo Marvin Turner
- Sun sace shi ne a gidansa da ke kan hanyar Samphino a Yenagoa, babban birnin jihar
- Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ya tabatar da faruwar al'amarin, ya ce ana kokarin ceto shi
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a daren ranar Lahadi sun sace Cif Gbalipre Turner, mahaifin Shugaban Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar Bayelsa, Hon. Ebinyo Marvin Turner.
An sace Cif Turner, wanda ya kuma kasance mamba mai ci a hukumar tara kudaden shiga ta jihar Bayelsa daga gidansa da ke kan hanyar Samphino a Yenagoa, babban birnin jihar.
Wata majiya daga iyalan ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa wasu ‘yan bindiga masu dauke da makamai na AK47 ne suka sace Turner, wanda shekarunsa ba su wuce 70 ba, da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi sannan suka tafi da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
'Yan bindigar ba su tuntubi iyalan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai taimaka wa shugaban karamar hukumar Ogbia, Johnson Ogbomade, wanda ya tabbatar da satar, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce jami'an rundunar sun kaddamar da farautar masu garkuwa da mutanen.
Ya ce:
“Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan wani Cif Gbalipre Turner a ranar 5 ga watan Satumba 2021, da misalin karfe 22:00, a Samphino Road, Yenagoa inda suka yi garkuwa da shi zuwa wurin da ba a sani ba.
"'Yan sanda sun amsa cikin gaggawa inda suka bi masu garkuwa da mutanen zuwa gabar ruwan Onuebum, inda suka yi watsi da motar da aka yi amfani da ita wajen yin garkuwa da guduwa da mutumin.
"Kwamishinan 'yan sandan jihar Bayelsa, CP Echeng E. Echeng, ya ba da umurnin bin sahu domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da cafke 'yan bindigar.
"Kwamishinan ya kara yin kira ga jama'a da su ba da sahihan bayanai masu amfani wadanda za su taimaka wa 'yan sanda a binciken da suke yi."
Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya
A wani labarin, iyayen daliban da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun koka kan rashin iya jin ta bakin masu garkuwa da mutanen da suka sace 'ya'yansu.
Rundunar ‘yan sanda ta ce an sace dalibai 73 lokacin da 'yan bindiga suka mamaye makarantar da misalin karfe 11 na safiyar Laraba da ta gabata.
Dalibai biyar, dukkansu 'yan mata, sun tsere daga hannun 'yan bindigan ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng