Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari Ya Shiga Ganawa da Shugabannin Tsaro a Fadarsa
- Shugaba Buhari ya shiga tattauna da shugabannin tsaron kasar nan a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja
- Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai hafsoshin soji, sufetan yan sanda da ministoci
- Wannan ya zo dai dai lokacin da ƙalubalen tsaro ke kara yawaita a Najeriya musamman a yankin arewa
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya shiga ganawa da shugabannin tsaron ƙasar nan a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.
Kakakin shugaban, Femi Adesina, ya rubuta a shafinsa na kafar sada zumunta Facebook, cewa Buhari zai amshi bayanai daga shugabannin tsaro kan halin da ake ciki.
Adesina yace: "Shugaba Buhari zai saurari bayanai game da tsaro a gidan gwamnati ranar 7 ga watan Satumba."
Legit.ng Hausa ta gano cewa shugaban zai karbi bayanai daga shugaban jami'an tsaro, Manjo Janar Lucky E. O Irabor, shugabannin hukumomin tsaro da suka haɗa da sufeta janar na yan sanda da sauransu.
Su wa suka halarci taron?
Daga cikin waɗanda suka halarci taron dake gudana yanzun haka sun haɗa da ministan tsaro, Bashir Magashi, da Ministan Shari'a, Abubakar Malami.
Sauran sun haɗa da ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama.
Ana tsammanin waɗanda suka halarci taron zasu baiwa shugaba Buhari bayanai game da yanayin tsaron da ake ciki a dukkan sassan Najeriya da kuma hanyoyin warware matsalolin.
Hotunan mahalarta taron
A wani labarin kuma Gwamna Masari Zai Katse Hanyoyin Sadarwa a Kananan Hukumomi 3 Na Jihar Katsina
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana shirin gwamnatinsa na datse hanyoyin sadarwa a wasu kananan hukumomi.
Masari yace waɗannan matakai da ake ɗauka zasu shafi mutane a hanyar cin abincinsu amma ya zama wajibi.
Asali: Legit.ng