Yan Kasuwa Sun Yi Fatali da Umarnin Gwamnatin Kaduna, Sun Koma Harkokinsu Kamar da a Kawo
- Yan kasuwar Kawo dake jihar Kaduna sun yi watsi da umarnin gwamnatin Kaduna na dakatar da cin kasuwar mako-mako
- Rahoto ya nuna cewa masu siye da masu siyarwa sun koma kasuwar ta Kawo jiya Talata ba tare da tunanin komai ba
- Wasu daga cikin yan kasuwar sun bayyana cewa suna sane da umarnin da gwamnati ta bayar
Kaduna - Yan kasuwa sun yi watsi da umarnin kulle da gwamnatin Kaduna ta saka a kasuwar Kawo, inda mutane suka cigaba da harkokin kasuwancinsu ranar Talata, kamar yadda premium times ta ruwaito.
Legit.ng hausa ta gano cewa gwamnatin Kaduna ta sanar da dakatar da kasuwar mako-mako, wanda ya haɗa babbar kasuwar Kawo a satin da ya gabata.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar.
Aruwan yace:
"Kasuwar kawo da mutane suka saba ci duk ranar Talata an dakatar da ita kuma umarnin zai fara aiki nan take."
Kasuwar kawo tana yanki ɗaya da makarantar horar da sojoji (NDA), kuma tana ɗaya daga cikin manayan kasuwanni a arewacin Kaduna.
Yan kasuwa sun cigaba da harkokinsu
Sai dai rahotanni sun nuna cewa dubbannin yan kasuwa da masu siyan kaya sun koma kasuwar ranar Talata, yayin da suka yi watsi da umarnin gwamnati.
Wakilin Premium times da ya ziyarci kasuwar domin ganewa idanunsa, ya ga mutane sun cigaba da harkokin kasuwancin su ba tare da damuwa ba.
Shin sun mance da umarnin gwamnati ne?
Wasu daga cikin yan kasuwar sun bayyana cewa suna sane da umarnin da gwamnati ta bayar na dakatar da cin kasuwa.
Wani mai siyar da doya yace:
"Ina kawo doya ta daga Zariya duk ranar Talata, na ji umarnin dakatarwar amma nasan ba za'a tilasta mana ba, shiyasa yau nazo cin kasuwa."
Wani jami'in ƙungiyar tsaron sa kai ta JTF ya bayyana cewa: "Masu siye da masu Siyarwa sun dawo kasuwar ne don su gane wa idon su irin tsaron da za'a saka."
A wani labarin kuma Cikin Sauki Sojoji Ke Maganin Yan Bindiga Tun Bayan Datse Sabis Na Sadarwa, Kwamishina
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, yace hare-haren da sojoji ke kaiwa kan yan bindiga ya fara haifar da ɗa mai ido.
Kwamishinan yace abun ya zo da sauki musamman bayan an datshe dukkan hanyoyin sadarwa na jihar.
Asali: Legit.ng