Niger: Mafarauta sun ragargaji ƴan bindiga, sun kashe 47 a Shiroro
- Mafarauta sun yi nasarar kashe yan bindiga kimanin guda 47 a kananan hukumomin Shiroro da Rafi a jihar Niger
- Mafarautan sun kai wa yan bindigan harin bazata ne a wani mabuyarsu da ke garin Magami suka yi nasarar cin galaba a kansa
- A baya-bayan nan ne Gwamna Abubakar Sani-Bello na jihar Niger ya kafa wata kungiyar yan banga na musamman don yakar yan bindigan
Mafarauta sun kashe a ƙalla ƴan bindiga 47 da ke adabar garuruwan da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Niger, PRNigeria ta ruwaito.
Mafarauta, yayin wani harin bazata da suka kai garin Magami da ke tsakanin ƙananan hukumomin Shiroro da Rafi, a ranar Laraba sun kashe yan bindigan a ranar Laraba.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa yan bindiga sun dade suna fakewa a garin da ke kusa da rafi.
Majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da kashe 'yan bindigan
Wani jami'in ɗan sanda na sirri wanda baya so a ambaci sunansa ya tabbatar cewa yan bindigan da dama sun tsere da raunin bindiga baya da waɗanda aka kashe.
Ya ce:
"Zan iya tabbatar maka cewa yan bindigan sun hadu da ajalinsu. Mafarautan sun kashe a ƙalla 47 daga cikinsu."
PRNigeria bata iya tabbatarwa ba ko mafarautan na cikin yan banga na musamman ta NSVC da gwamnatin jihar Niger ta kafa a jihar don tallafawa hukumomin tsaro.
Yayin rantsar da su a Yunin 2021, Gwamna Abubakar Sani-Bello na jihar ya ce ba za su bari ƴan bindigan su yi musu barazana ba ko su sauya musu tsarin rayuwarsu.
Mr Sani Bello ya ce:
"Yan bindigan suna son tilasta mana sauya tsarin rayuwarmu a Jihar Niger amma ba za mu ƙyalle su ba.
"Sun hana yaran mu zuwa makaranta, sun hana mu tafiya a tituna, sun hana manoma zuwa gonaki yanzu suna neman hana mu komai, amma ba za mu gajiya ba. Ba za mu bari hakan ya faru ba; za mu cigaba da rayuwar mu yadda muka saba."
Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar
A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.
Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng