Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna

  • Alhaki ya kama wasu kungiyoyin ‘yan bindiga biyu a karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna
  • Batakashi ya barke tsakaninsu inda hakan yayi sanadiyyar halakar mutane 9 cikin ‘yan ta’addan
  • Rahotanni sun tabbatar da yadda sukayita yi wa juna aman wuta sakamakon kulalliyar gabar da ke tsakaninsu

Giwa, Kaduna - Alhakin jama’a ya kama kungiyoyi biyu na wasu shu’uman ‘yan bindiga a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna inda harbe-harbe ya barke tsakaninsu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Rikicin ya yi sanadiyyar halakar mutane 9 a cikinsu kamar yadda jami’an binciken sirri suka tabbatarwa da gwamnatin jihar Kaduna.

Alhaki: Ƴan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin ɓangarori biyu da basu ga maciji a Kaduna
Taswirar Jihar Kaduna. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Ku Tuba Ku Miƙo Makamanku, Ko Ku Fuskanci Ƙalubale, Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Zamfara

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar da hakan a ranar Juma'a.

Kwamishinan tsaro na Kaduna ya tabbatar da lamarin

Aruwan ya bada labarin yadda kazamin fadar ya faru tsakanin yan bindigan a ranar Laraba

Ya ce:

"Rahotanni sun bayyana yadda wani hatsabibin dan bindiga wanda akafi sani da ‘Godon Mota’ ya afka kauyen Garke a ranar Laraba tare da yaransa suka ci karo da wasu ‘yan bindigan da basa ga maciji.
"Haduwarsu ke da wuya suka fara batakashi wanda hakan yayi sanadiyyar kassara mutane 9 a cikinsu."

Duk da dai har yanzu ba a samu kwakkwaran dalili ba akan rashin ga-macijin kungiyoyin guda biyu ba amma ance sanadiyyar samun sabani ne akan raba wani kudin fansa wanda wasu daga cikin kungiyar suke ganin kamar an cucesu.

Abin da mataimakiyar gwamnan Kaduna ta ce game da lamarin?

Gwamnan rikon kwarya na jihar, Dr Hadiza Balarabe ta yi farin cikin aukuwar lamarin kuma ta umarci jami’an tsaro da suyi kokarin ganin sun kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da ke yankin cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Kisan Filato: Duk wanda ke gaggawar karbar belin wanda ake zargi za a kwamushe shi, Lalong

Ana cigaba da bincike kan lamarin kana jami'an tsaro na sintiri a yankin.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma da yan bindiga da masu garkuwa suka addabi mutanen gari da dalibai a makarantu.

Ƴan Bindiga Sun Kutsa Makarantar Islamiyya Sun Sace Ɗalibai a Katsina

A wani labarin daban, kun ji cewa Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukan darrusa a harabar makarantar da yamma.

A halin yanzu ba a kammala tattaro bayannan yadda lamarin ya faru ba kuma ba a san inda aka tafi da wadanda aka sace din ba a lokacin hada wannan rahoton.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel