Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari

Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa mulkinsa zai tabbatar da kulawa da rayuka da dukiyoyin su
  • Ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce shugaban kasa ya bayyana wannan tabbacin ne a wani taro na tsaron kasa da suka yi a fadarsa da ke Abuja
  • Magashi ya bayyana yadda shugabannin tsaro suka bayyana wa shugaban kasa halin da kasar nan ta ke ciki da sabon harin da aka kai wa jihar Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da ‘yan Najeriya tabbacin sa na cewa mulkin sa zai tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin duk wasu ‘yan Najeriya ko menene matsayinsa a kasar nan.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ministan tsaro, Bashir Magashi ya ce Shugaban kasa ya bayyana hakan a wani taro na tsaron kasa wanda suka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, Buhari
Mulki na ya shirya bai wa rayuka da kadarorin 'yan Najeriya kariya, cewar Buhari. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Magashi ya bayyana hakan inda yace shugabannin tsaro sun kara bayyana halin da kasar nan ta ke ciki na rashin tsaro har da sabon ta’addancin da ya faru a jihar Zamfara da sauran jihohi na arewa maso yanma da arewa ta tsakiya da ke fadin kasar nan, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

“An yi taron ne musamman don bayyana halin da arewa maso yamma da arewa ta tsakiya ta ke ciki na matsaloli da sauran ta’addanci na garkuwa da mutane da sauran su.
“Daga taron, mun yarda da cewa hakkin gwamnati ne kawo karshen ta’addanci da ke faruwa a jihar Zamfara da arewa ta tsakiya.
“Mun tattauna a kan bukatar kawo karshen ‘yan ta’adda. Mun yarda da cewa suna kawo cece-kuce, hallaka jama’a, suna yin yadda suka ga dama kuma suna fadin abubuwan da suka so don su samu duk abinda suke so a hannun jama’a.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki

“Mun yarda da cewa muna iyakar kokarinmu na ganin mun dunkule kasar nan waje guda. Idan aka dubi shekarar 2014, za ka gane cewa an samu cigaba mai tarin yawa amma mutane ba sa ganin hakan.
“Gani suke yi kamar mun gaza ko kuma akwai wasu abubuwan da ba mu sani ba. Muna iyakar kokarin mu amma mutane ba sa ganin kokarin gwamnati.
“Mun san abinda muke yi kuma mun gane cewa za mu iya tsare Najeriya amma muna bukatar hadin kai.
“Kamar yadda kowa ya sani duk kasar da babu tsaro ba za ta iya tabuka komai ba. Don haka ya umarce mu da mu nemi hanyoyi da dabarun da za mu kawo karshen rashin tsaro kuma mun tabbatar masa da cewa za mu yi iyakar kokarin mu a kan lamarin,” a cewarsa

Ce musu na yi ina da aure: Macen Kirista mai zaman zuhudu da aka sace yayin harbin Sowore ta bada labari

Kara karanta wannan

Rashin kwazo: An gano sahihan dalilan da suka sa Buhari ya sallami Nanono da Mamman

A wani labari na daban, Reverend Sister Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna kashe kanin Omoyele Sowore, kanin mai Sahara Reporters, ta bayyana yadda ta tsere daga hannun su.

Daily Trust ta ruwaito cewa, sun harbe kanin Sowore har lahira ya na hanyarsa ta zuwa jami’ar Igbinedion Okada da ke jihar Edo a ranar Asabar.

Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, sun harbe shi ne yayin da ya yi yunkurin tserewa daga masu garkuwa da mutanen da ke kan titin Benin zuwa Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng