Ce musu na yi ina da aure: Macen Kirista mai zaman zuhudu da aka sace yayin harbin Sowore ta bada labari

Ce musu na yi ina da aure: Macen Kirista mai zaman zuhudu da aka sace yayin harbin Sowore ta bada labari

  • Reverend Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna sheke kanin Sowore, ta bayyana yadda ta tsere daga wurin su
  • Ayanwu ta bayyana yadda ta ke hanyar ta zuwa jihar Imo sai suka tsayar da su a jihar Legas, inda ta hau motar da za ta kai ta, babbar matsalar ta faru ne bayan motar ta lalace
  • Ta bayyana yadda ta tsere ofishin ‘yan sanda cikin gaggawa a lokacin da ta ga hankalin masu garkuwa da mutanen ya karkata a kan wasu mutanen da suka sata

Edo - Reverend Sister Emmanuella Ayanwu mai shekaru 34, daya daga cikin mutane 5 da masu garkuwa da mutane suka sata har suna kashe kanin Omoyele Sowore, kanin mai Sahara Reporters, ta bayyana yadda ta tsere daga hannun su.

Kara karanta wannan

Yadda matashi a Gombe ya dale karfen sabis ya ce ba zai sauko ba sai an masa aure

Daily Trust ta ruwaito cewa, sun harbe kanin Sowore har lahira ya na hanyarsa ta zuwa jami’ar Igbinedion Okada da ke jihar Edo a ranar Asabar.

Ce musu na yi ina da aure: Macen Kirista mai zaman zuhudu da aka sace yayin harbin Sowore ta bada labari
Macen Kirista mai zuhudu tace wa miyagun da suka sheke Sowore tana da aure. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, sun harbe shi ne yayin da ya yi yunkurin tserewa daga masu garkuwa da mutanen da ke kan titin Benin zuwa Legas.

Ayanwu wacce ke tafe da kariyar Ubangiji ta bayyana yadda ta ke hanyarta ta zuwa jihar Imo sai ta tsaya a Legas inda ta hau motar da za ta kai ta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta, matsalar ta auku ne lokacin da motar ta samu matsala, Daily Trust ta wallafa.

Ta bayyana yadda ta shige ofishin ‘yan sanda bayan ta ga hankalin masu garkuwa da mutanen ya karkata daga kan ta.

“Ana ruwan sama da misalin karfe 7:30 na dare sai suka turo wata mota ta dauke mu a daji. Suka amshi wayar mutumin da sauran abubuwa.

Kara karanta wannan

Harin NDA: Rundunar sojin Najeriya ta ki bayyana halin da Manjon da aka sace ya ke ciki

“Sai na lura da cewa hankalinsu ya karkata a kan mutumin, sai na cire kyallen da suka rufe min ido da shi na lallaba na gudu ba tare da sun lura ba.
“Bayan na isa kan titi sai na hadu da wani mutum da ya nuna min wasu ‘yan sanda a bakin titin masu babura bayan na bashi labari na.”

Daga nan ne suka kai ni ofishin su da ke Benin, babban birnin jihar Edo.

Batun yadda suka sace ta tace:

“Maza 5 ne suka bayyana daga cikin daji bayan motar mu ta samu matsala suka fara harbe-harbe.”

Ta ce, take a nan suka zagaye su sannan suka umarci kowa ya fito daga abin hawansa kuma ya kwanta sannan suka rufe musu idanunsu bayan sun kwace musu duk wasu abubuwan su masu daraja.

“Sun tambayeni idan na yi aure sai na fada musu cewa ina da aure har da yara 2 amma ba gaskiya ba ne saboda irin mu ba mu aure,” a cewar ta.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

A wani labari na daban, tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a minista bayan ganin takardun sa bai wuci da sa’o’i biyu ba.

Daily Nigerian ta ruwaito hakan ne bayan kwanaki kadan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami ministan wutan lantarkin da kuma ministan ayyukan noma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel