Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

  • Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, ya bayyana yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a minista kafin ya kai sa’a biyu da amsar takardun sa
  • A ranar Laraba da ta gabata, shugaban kasa ya sauke shi daga mukaminsa da takwaransa a mukami, ministan noma, Alhaji Muhammad Sabo Nanono
  • Mamman ya bayyana yadda zai ci gaba da yi wa shugaban kasa fatan alkhairi da ya zabe shi a matsayin minista ba tare da ya yi ta rokon sa ba

Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a minista bayan ganin takardun sa bai wuci da sa’o’i biyu ba.

Daily Nigerian ta ruwaito hakan ne bayan kwanaki kadan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami ministan wutan lantarkin da kuma ministan ayyukan noma.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman
Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman ya ce bayan sa'o'i 2 da karbar takardun sa Buhari ya nada shi minista. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
“Zan cigaba da yi wa shugaban kasa godiya saboda zabe na da yayi ba tare da na roke shi ba. Bai kai sa’a biyu ba da ya amshi takardu na ya nada ni a matsayin minista,” a cewar tsohon ministan.

Ya musanta yadda mutane suka yi ta yada cewa bayan ya samu labarin tube shi daga mukamin sa ya fadi aka nufi asibiti da shi. A cewar sa, ya je asibiti ganin likita ne aka sanar da labarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce shugaban kasa ya bayyana masa cewa zai cire shi daga mukamin sa, Daily Nigerian ta wallafa hakan.

“Na ji mutane suna cewa na fadi bayan jin labarin an cire ni daga mukamin. Na bar duk masu yada labarin nan da Allah.
“Na san lafiya ta kalau. Wadanda suka ce na fadi su sanar da wurin da na fadi da kuma inda aka kai ni.

Kara karanta wannan

Korar minostocin Buhari: APC ta ce a maye gurbin Sale Mamman da dan jihar Taraba

“Da farko da mutane suna ta fargaban sanar da ni labarin, ba su san Shugaban kasa ya fada min tun farko ba,” a cewar sa.

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam'iyyar baki daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da rasa mambobin ta.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce tuni ya nisanta kan sa daga dukkan wani rikici kuma kamar yadda ya ce, wadanda ba kwararrun 'yan siyasa ba ne suka hura wutar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel