Rashin kwazo: An gano sahihan dalilan da suka sa Buhari ya sallami Nanono da Mamman
- Jiya shugaban kasa ya sauke ministan noma da habaka karkara da kuma ministan wutar lantarki yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya
- Buhari ya lashi takobin ci gaba da sauya wa ministocin ma’aikatu don yanzu haka akwai wadanda ake shirin saukewa ko kuma canja wa matsayi
- Bincike ya tabbatar da cewa shugaba Buhari ya zargin Nanono da Mamman da rashin kwazo a bangaren da ya saka su na noma da wutar lantarki
Hankula sun tashi tun bayan ganin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauke ministocinsa guda biyu daga majalisarsa kamar yadda Daily Trust ta gano.
A jiya, shugaban kasa ya sanar da korar ministan noma da bunkasa karkara, Alhaji Sabo Nanono da kuma ministan wutar lantarki, Injiniya Sale Mamman yayin taron majalisar zartarwa a karshen kowanne mako.
Wannan ne karo na farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tauna aya don tsakuwa ta ji tsoro tunda ya hau mulki a 2015. Ya dawo ya cigaba da ayyuka tare da ministocinsa tun na farko da aka zabe shi a 2015.
Daily Trust ta ruwaito yadda Nanono da Mamman suka kasance abokan Buhari wadanda suka dade sosai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An maye gurbin ministocin da ministan muhalli, Dr. Mohammad Mahmood Abubukar da kuma karamin ministan gidaje da ayyuka, Injiniya Abubakar D. Aliyu.
Fadar shugaban kasa ta bai wa Daily Trust bayanai jiya cewa akwai sauran ministocin da za a sauke daga yanzu zuwa ko wanne lokaci.
Shugaban kasa ya tabbatar da cewa zai cigaba da sauya wa ministocin ma’aikatu a kowanne taron majalisar zartarwa.
Masu kusanci da Buhari sun ce ya yi magana mai harshen damo inda yake gwada cewa wajibi ne kowa ya dinga bayyana ayyukan ma’aikatarsa a gaban majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da kuma gudunmawar da ya ke bayarwa.
Sannan baya ga bukatar bunkasa ma’aikatu, akwai bukatar su bayyana wa ‘yan Najeriya abinda ma’aikatunsu suke ciki kamar yadda shugaban kasa ya bukata, sannan akwai majiyoyi da suke nuna cewa ministocin da Buhari ya sauke basu tabuka wasu ayyuka a ma’aikatunsu.
Hadimin shugaban kasar wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya ce gabadaya shugaban kasan ya lura basu tabuka abin azo a gani shiyasa ya yanke shawarar maye gurbinsu.
Shugaban kasa ya canja su da mutane biyu da yake tunanin za su fi su aiki. Ana tsammanin Mamman din Taraba zai tabbatar da aikin wutar lantarki ta Mambila sakamakon shi asalin dan can ne, amma har yanzu ba a samu hakan ba.
A kuwa kwarewar Alhaji Muhammad Sabo Nanono, an yi tsammanin cewa za a ga manyan ayyuka da bunkasa harkar noma a karkashinsa.
'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa
A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da sheke wani mai garkuwa da mutane da 'yan banga suka yi yayin da ya je karbar kudin fansa daga 'yan uwan wacce ya sace, Daily Nigerian ta ruwaito.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a Yola, ya ce lamarin ya faru a ranar 26 ga watan Augusta a karamar hukumar Song ta jihar.
"Rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahoto daga 'yan sandan Song a ranar 26 ga watan Augusta kan cewa 'yan banga sun sheke wani da ake zargi da garkuwa da mutane yayin karbar kudin fansa," Nguroje ya ce.
Asali: Legit.ng