An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun

An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun

  • Cutar kwalara ta ɓarke a Ogun, inda aka tabbatar da ta kashe aƙalla mutum 25 a Magboro, karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar
  • Barkewar cutar ta shafi garuruwan Arepo, Akeran, Akintonde, Sofolarin da Abule - Oko na Magboro
  • Kwamishinar lafiya, Dr Tomi Coker, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, ya fi yawa a tsakanin masu kabu-kabu a yankin

Mutane 25 ne ake fargabar sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a Magboro, karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa barkewar cutar ta shafi garuruwan Arepo, Akeran, Akintonde, Sofolarin da Abule - Oko na Magboro, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna garin.

An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun
An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Kwamishinar lafiya, Dr Tomi Coker, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, "ya fi yawa a tsakanin masu kabu-kabu a yankin."

Shugaban Kwamitin Ci gaban Al'umma a Magboro, Oluwasegun Oladosu, ya shaida wa jaridar a ranar Talata cewa an samu asarar rayuka 15.

Ya kara da cewa kusan mutane 10, wadanda suka tashi daga garin zuwa Kara suma sun mutu sanadiyar cutar kwalara.

Oladosu ya ce masu sana’ar tuka babura sun fi kamuwa da cutar. Ya kuma ce an garzaya da yarinya ‘yar shekara takwas da ke fama da cutar kwalara zuwa asibitin al’umma domin yi mata magani.

Shugaban na CDC ya ce wata tawagar gwamnati ta ziyarci garin kuma ta ba da magunguna don maganin kwalara da rigakafin cutar.

Sai dai kuma ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa a koda yaushe tana aiwatar da shirin tsaftace muhalli a cikin al'ummar Hausawa, wanda ya yi wa lakabi da "mara tsafta."

Cutar Kwalara Na Kara Yaduwa a Fadin Najeriya Yayin da Ta Kashe Sama da Mutum 146 a Jihar Kebbi

A gefe guda, akalla mutun 146 sun rasa rayukansu a jihar Kebbi, a cewar wani jami'in lafiya yayin da cutar kwalara da ta ɓarke a Najeriya ta shiga jihar.

Premium times ta ruwaito yadda cutar kwalara wacce take jawo amai da gudawa take kara cin karenta babu babbaka a Najeriya, inda abun yafi muni a yankin arewa maso yamma.

Cutar ta kashe mutun 75 a jihar Katsina zuwa ranar Talata, yayin da ta kashe 30 a Zamfara, 23 a Sokoto da kuma mutum 119 a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel