Da dumi-dumi: 'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore

Da dumi-dumi: 'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore

  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kisan kanin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan Edo, Kontongs Bello, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe Olajide a safiyar yau a Asabar
  • Ya kuma ce sun kuma yi garkuwa da wasu mutane biyar, inda yace ana kokarin ceto su

Edo - Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan Felix Olajide Sowore, kanin mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.

Jaridar The Nation ta ruwaito Sowore, a wani sako da safiyar ranar Asabar, ya ce wasu da ake zargin makiyaya / masu garkuwa da mutane ne sun kashe dan uwansa a jihar Edo.

Da dumi-dumi: 'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore
'Yan sanda sun tabbatar da kashe dan uwan Sowore
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ‘yan sandan Edo, Kontongs Bello, ya ce masu garkuwa da mutane sun kashe Olajide da misalin karfe 6:00 na safiyar Asabar, jaridar ta kuma ruwaito.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: IGP Baba ya bayyana yadda ya zama shugaban yan sanda a mawuyacin lokaci

Hakazalika ya bayyana cewa sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a yayin harin, jaridar Daily Trust ta ruwaito

“Wannan don tabbatar muku da cewa wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne da misalin karfe 06:45 na safiya a hanyar Legas zuwa Benin ta hanyar Isuwa sun yi garkuwa da mutane biyar da ba a san ko su wanene ba sannan a cikin lamarin sun harbi wani Sowore Felix Olajide, dalibin karatun hada magunguna na Jami’ar Igbinedion Okada.
“An ajiye gawarsa a IUTH dakin ajiye gawa na Okada yayin da ake ci gaba da kokarin ceto mutane biyar da aka yi garkuwa da su. Ana ci gaba da aikin bincike da ceto.”

Yan bindiga sun kashe Kanin Mai Sahara Reporters, Sowore

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun kame fatun Jakuna da ake kokarin fitar wa kasar waje

A baya mun kawo cewa Yan bindiga sun bindige Olajide, wanda kani ne ga mai gidan jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, har lahira.

Sowore ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar.

Dan jaridan ya bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kasheshi a hanyarsa daga jami'ar Igbinedion dake garin Okada, jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel