Labari mara dadi: 'Yan fashin daji sun sheke 'yan banga 2 a jihar Niger

Labari mara dadi: 'Yan fashin daji sun sheke 'yan banga 2 a jihar Niger

  • 'Yan bindigan daji a jihar Niger sun sheke 'yan banga 2 a yayin wata arangama da suka yi
  • Mummunan lamarin ya auku ne a yankin Mayaki da ke karamar hukumar Lapai ta jihar Niger
  • Shugaban 'yan sintirin jihar ya ce jami'ansu sun bi sahun miyagun domin damko su

Niger - Sakamakon musayar ruwan wuta tsakanin miyagun 'yan bindigan daji da 'yan banga da aka yi a yankin Mayaki da ke karamar Lapai ta jihar Niger, 'yan banga 2 sun rasa rayukansu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mayaki na da iyakoki da Gwaji, wani yanki na karamar hukumar Abaji da ke babban birnin tarayya.

Labari mara dadi: 'Yan fashin daji sun sheke 'yan banga 2 a jihar Niger
Labari mara dadi: 'Yan fashin daji sun sheke 'yan banga 2 a jihar Niger. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mazauna yankin sun ce, lamarin ya auku a ranar Lahadi wurin karfe 10:23 na safe yayin da wasu 'yan banga suka fita sintiri kuma miyagun 'yan bindiga suka biyo su a yankin.

Kara karanta wannan

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana kansa da suna Ahmadu, ya ce 'yan banga sun yi musayar ruwan wuta da miyagun inda suka sheke 'yan banga biyu har lahira.

Ya ce daga bisani 'yan bindigan sun tsere bayan sun gano cewa 'yan bangan kauyen Kapako sun fara kokarin bayyana, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamandan 'yan sintiri na jihar Niger, yankin Lapai, Muhammadu Ibrahim, ya tabbatar da mutuwar 'yan bangan biyu.

"Tabbas mu rasa mutum biyu daga cikin jami'anmu a yayin wani sintiri da suka fita wurin dajin Mayaki," yace.
"A yanzu da muke magana da ku, mun tura jami'anmu kuma sun fara farautar 'yan ta'addan da suka yi aika-aikar," ya kara da cewa.

Ba mu da hannu cikin kashe-kashen matafiya a Jos, Matasan Irigwe sun magantu

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja

A wani labari na daban, Kungiyar cigaban Irigwe, wata kabila ta jihar Filato a ranar Litinin ta musanta zargin mutanenta da hallaka rayuka 22 na matafiya a tititin Rukuba da ke Jos a ranar 14 ga watan Augusta.

Shugaban kungiyar, Robert Dodo ya musanta zargin a wani taro da suka yi a Abuja. A cewar Dodo, mutanen sa suna cikin masu alhinin faruwar lamarin kuma suna cikin wadanda suka birne jama’an bayan ‘yan bindigan sun tafka aika-aikar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a cewar sa sai da mutanen yankin suka nemi izinin ‘yan sandan Jos wadanda suka samar da tsaro yayin birniyar. Ya kara da cewa, ‘yan sandan sun bai wa masu makokin shawarar kada su bi ta titin Rukuba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel