Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja

  • Bayan hallaka musu mutum 40, yan bindiga sun kai ramuwar gayya
  • Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu yayinda da dama sun jikkata
  • Mutan garin na kira ga gwamnati ta kawo musu dauki

Jihar Neja - Yan bindiga a daren Juma'a su kai mumunan hari garin Magami dake karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja inda suka hallaka mutum akalla 20 lokaci guda.

Sakamakon wannan hari, mutan garin sun gudu daga muhallansu zuwa wasu garuruwa.

Mazauna garin sun ce wannan ramuwar gayya ce yan bindiga suka kai don an kashe musu yan'uwa yan bindiga a garin.

Zaku tuna cewa a daren Laraba, gamayyar jami'an tsaro da ya hada da yan sanda, mafarauta, da yan banga sun kaiwa yan bindiga hari inda suka kashe mutum 40 cikinsu kuma suka kwashe makamai da babura.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

Kakakin kungiyar Matasan Shiroro, Mallam Yusuf Abubakar Kukoki, wanda ya tabbatar da kisan ya bayyanawa DailySun cewa yan bindigan sun dira garin da yawansu.

Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja
Da duminsa: Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja
Asali: UGC

A cewarsa:

"Yayinda suka lura cewa gamayyar jami'an tsaron da suka kai musu hari sun koma Galadima Kogo, yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya inda suka kashe duk wanda suka gani."
"Bisa kirgen da da akayi, akalla mutane 15 yan bindigan suka hallaka. Mutum 6 a Unguwar Magiro a karamar hukumar Rafi, mutum hudu a Farin Hula da mutum biyar a Magami, karamar hukumar Shiroro yayinda mutanen da yawa sun bace."

Kukoki ya kara da cewa mutanen garuruwan da dama sun gug hedkwatar karamar hukumar Kuta don neman mafaka.

Gwamnatin Niger ta rufe kasuwannin shanu, ta takaita yawo a babura

Kara karanta wannan

Mutum uku sun mutu yayin da miyagun Yan bindiga suka kai sabon hari jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Neja ta dakatar da cin kasuwar shanu ta kowanne mako a fadin jihar a matsayin hanyar magance hauhawar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana wannan sanarwar ne ta wata takarda ta ranar Talata inda ya ce wajibi ne duk wani abin hawa da ke dauke da shanu da zai shiga cikin jihar ya nuna takardar shaida da alamar inda aka siyo shanun da kuma inda za a kai su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel