Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

  • Jirgin yakin dakarun sojin Najeriya na sama ya ragargaji wani sansanin kuma ma'adanar 'yan bindiga a dajin Kawara, jihar Kaduna
  • Jirgin yakin ya hango miyagun tare da shanun sata sanye da bakaken kaya, hakan yasa aka harba musu bama-bamai da suka tashi da su
  • Jirgin ya hango wata ma'adanarsu inda ya jefa bam ta kone babura tare da kayan abinci, an samu gawawwaki a kalla 50 na miyagun

Kaduna - A sakamakon tashi tsaye da gwamnati ta yi wurin kawo karshen ta'addanci a wasu jihohin arewa, dakarun soji suna ta kai da kawowa tsakanin Zamfara zuwa wasu jihohi a cikin kwanakin nan.

Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kone wani sansanin 'yan fashin daji da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda PRNigeria ta tattaro, miyagun suna amfani da sansanin wurin buya a dajin Kawara da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara
Jirgin yakin NAF da ya ragargaji sansanin 'yan bindiga a dajin Kawara da ke jihar Kaduna. Hoto daga PRNigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi sun kara da cewa, a kalla 'yan fashin daji 50 bandits sun sheka lahira bayan bama-baman da dakarun suka sakarwa miyagun, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda wata majiya ta cikin dakarun sojin saman ta sanar, jirgin yakin NAF ya tare wasu tarin 'yan fashin daji da ke sanye da bakaken kaya kuma sun sato shanu wurin kauyen Kawara a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

"Bayan sun hango jirgin yaki, 'yan bindigan sun tsere tare da boyewa cikin shanun yayin da suke neman hanyar gudu.
“Bayan hadewa da suka yi a wurin wani ruwa za su tsallaka, an yi nasarar jefa musu bam ta jirgin yakin.
"An hango gawawwakin wasu daga cikin 'yan fashin dajin yayin da wasu da ke kokarin tserewa aka sake sakar musu bam.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

“Bayan an sake duba daga inda suka fito, an hango wani sansani da suke adana kayan ayyukansu wanda aka sakar masa bam ya kone kurmus.
“Majiyoyi daga kasa a Kawara a ranar Litinin sun tabbatar da cewa a kalla gawawwakin miyagu 50 aka kirga yayin da aka tsinci babura da kayan abinci konannu a sansanin," ya ce.

'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara

A wani labari na daban, Badawi Abdullahi Ahmed matashi ne mai shekaru 38 wanda ake zargi da zama gagarumin barawon motoci a Abuja kuma rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya suka yi ram da shi a Zamfara.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami'an 'yan sanda daga Maitama suka bibiye shi har zuwa Talata Mafara da ke jihar Zamfara inda suka kama shi tare da abun hawan da ya sata.

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, Daniel Ndirpaya, ya ce Abullahi kwarrare ne wurin satar motoci a ma'adanar su.

Kara karanta wannan

Atiku: Ya kamata a kirkiri rundunar 'yan sandan da aikinta shine gadin makarantu

Asali: Legit.ng

Online view pixel