Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

  • Kungiyar dattawan arewa, NEF, ta ce ba ta sukar matakan tsaro da yaki da 'yan bindiga da gwamnati ta dauka
  • Hasalima, kungiyar ta jinjinawa gwamnonin jihohin na arewa tare da rokar gwamnatin tarayya da ta basu tallafi
  • NEF ta bukaci gwamnatocin jihohin arewa da su samar da isasshen tsaro ga yankunan da ake yi wa 'yan bindiga lugude

Zauren dattawan arewa, NEF, a ranar Litinin ya ce ba ya sukar matakan tsaron kasa da wasu gwamnonin jihohin arewa maso yamma suka dauka da jihar Niger domin dakile miyagun hare-haren 'yan ta'adda.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnonin sun dakatar da kasuwannin da ake ci duk mako tare da hana siyar da fetur a jarkoki da kuma sauran hanyoyin dakile matsalolin tsaro a jihar.

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa
Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce NEF ba ta sukar matakan tsaron gwamnati. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A wata takarda ta ranar Lahadi, daraktan yada labarai na kungiyar, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce dukkan matakan da aka dauka za su iya sa miyagun su sake balle ta'addanci a yankunan da babu tsaron.

Kara karanta wannan

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

A yayin zantawa da Daily Trust a ranar Litinin, Baba- Ahmed ya kara haske inda ya ce NEF ta na goyon bayan matakan da aka dauka, kawai ta janyo hankalin gwamnatocin ne kan abinda zai iya faruwa da yankunan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce kada a bar yankunan haka kawai a hannun 'yan ta'adda bayan an garkame su tare da saka musu dokar ta baci.

Ya yi kira ga gwamnatoci da su dinga duba halin da yankunan suke ciki tare da tabbatar da daukar matakan tsaro.

"Ba mu kushe matakan tsaron da gwamnatocin jihohi suka dauka na kayyade wasu al'amuran kamar kasuwanci, sadarwa da makarantu ba. Abinda ya ce mu yi shi ne mu tabbatar da cewa wadannan matakan suna amfani wurin batar da miyagun tare da datse ayyukansu a yankunan karkara," yace.

Ya kara da jaddada cewa, dukkan jihohin da aka sakawa dokokin ta-bacin, ya dace su samu tallafi da taimako daga gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan bindiga sun gurzu, suna rokon jama'a yafiya tare da sako wadanda suka sace a Zamfara

'Yan sanda sun yi ram da gagarumin barawon motoci na Abuja a Zamfara

A wani labari na daban, Badawi Abdullahi Ahmed matashi ne mai shekaru 38 wanda ake zargi da zama gagarumin barawon motoci a Abuja kuma rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya suka yi ram da shi a Zamfara.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, jami'an 'yan sanda daga Maitama suka bibiye shi har zuwa Talata Mafara da ke jihar Zamfara inda suka kama shi tare da abun hawan da ya sata.

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, Daniel Ndirpaya, ya ce Abullahi kwarrare ne wurin satar motoci a ma'adanar su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng