Nasara: 'Yan bindiga na roko jama'a su yi wa gwamnati bore, sun fara sako wadanda suka sace a Zamfara

Nasara: 'Yan bindiga na roko jama'a su yi wa gwamnati bore, sun fara sako wadanda suka sace a Zamfara

  • Luguden wutan da sojin sama da na kasa suke yi a jihar Zamfara tare da tsuke bakinsu yana fitar da sakamakon da ake bukata
  • Tuni 'yan bindiga sun fara rokon mazauna jihar da su bijirewa gwamnati, tare da alkawarin cewa za su tuba idan hakan ta faru
  • Har ila yau, jama'ar da suka yi watanni da makonni a wurin miyagun sun fara dawowa gida saboda azabar da 'yan fashin dajin ke ciki

Zamfara - Shugabannin 'yan bindiga masu tarin yawa da yaransu sun sheka barzahu a yayin luguden wutan da ake yi a jihar Zamfara, majiyoyi masu tarin yawa suka sanar da Daily Trust a jiya.

An gano cewa dakarun sojin kasa tare da hadin guiwar na sama ne ke ta luguden wutan tun bayan da aka datse hanyoyin sadarwa a jihar tare da saka dokar kulle.

Kara karanta wannan

Yakar 'yan bindiga: Ba mu sukar matakan tsaro da gwamnati ta dauka, Dattawan Arewa

Daya daga cikin majiyoyin, wanda jami'in soja ne, ya ce an samu manyan nasarori a wannan samamen da ake ta kaiwa miyagun 'yan fashin daji a jihar Zamfara da kewaye.

Nasara: 'Yan bindiga suna shan wuta, sun fara sako wadanda suka sace a Zamfara
Gwamna Bello Matawalle ya ce zai zauna a jihar har sai an kammala aikin da jami'an tsaro ke yi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Aiki ake yi, babu surutu

Duk da gwamnatin tarayya ba ta datse hanyoyin sadarwa na jihohin Katsina, Kaduna da Niger ba, majiya kusa da jami'an tsaro da na sirri ta ce an bukaci jami'ai da su tunkari 'yan bindigan a jihohin ba tare da shelanta aikinsu ba.

"Sojoji, 'yan sanda da jami'an DSS duk an umarce su da su tsuke bakunansu a kan wannan aikin ta yadda za a hana masu kaiwa 'yan fashin dajin bayanai damar kai labarin abinda za a yi," yace.

'Yan bindiga sun fara rokon jama'a da su bijire wa gwamnati

Kara karanta wannan

Daga Zamfara zuwa Kaduna: Jirgin yakin NAF ya kone sansanin 'yan bindiga, an kashe 50 a dajin Kawara

Wani mazaunin Zamfara mai suna Mahe Musa, wanda ya samu damar zantawa da Daily Trust yayin da ya je Funtua, ya ce 'yan bindigan sun fara rokon jama'a da su bijirewa gwamnati ta hanyar yin zanga-zanga.

"An saka 'yan bindigan a lungu daya, ba su jin dadin lamarin," yace.
"A halin yanzu, ba su samun komai saboda basu da iko da ko ina. Sun fara rokon jama'a da su yi wa gwamnati zanga-zanga ta yadda za a dage dokokin hana yawo, siyar da fetur da kuma shanu.
“Sarakunan gargajiya da na addinai su ke wayar wa da jama'a kai a kan kada su yi bore, ba za mu saurari 'yan fashin daji ba," ya ce.

Dole ta sa 'yan fashin daji sun fara sakin wadanda suka sace

Gwamna Matawalle a ranar Litinin, ya ce dole ta sa 'yan fashin daji sun fara sakin wadanda ke hannunsu saboda ba su iya ciyar da su kuma ba su samun abinci, mai da sauran hanyoyin sadarwa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Kamar yadda Matawalle ya ce, jama'an da suka kwashe makonni da watanni a hannun miyagun duk sun fara komawa gida kuma miyagun suna ta yadda baburansu saboda rashin mai.

FG za ta karbo miliyoyin naira da ta tura wa likitoci 588 bisa kuskure

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya za ta amso miliyoyin nairorin da ta biya likitoci 588 da ke fadin kasar nan bisa kuskure.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige ne ya bayyana hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran gidan gwamnati a Abuja.

Ya bayyana yadda kudaden suka shiga asusan likitoci na daban maimakon na likitoci masu neman kwarewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel