Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai

Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai

  • Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya bayyana cewa matsalar garkuwa da mutane ta fi shafar Fulani
  • Bagudu ya sanar da cewa hatta satar shanu da ake cewa suna yi, ta fi shafar su, kawai ba a sauraron su ne
  • Gwamman ya ce ya zagaya yankunan Fulani a jiharsa inda ya ji kokensu, babu shakka ta kansu komai ya fara

Kebbi - Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi, ya ce matsalar garkuwa da mutane tare da satar shanu a kasar nan ta fi shafar Fulani.

A yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Bagudu ya ce jama'a ba su sauraron abinda Fulani ke fuskanta a bangare garkuwa da su ko kuma sace musu shanu.

Kara karanta wannan

Sace dalibai 73 a Zamfara: ACF ta dau zafi, ta ce duk gwamnatin da ba za ta kare al’umma ba bata da amfani

Bagudu: Muguntar 'yan bindiga ta fi shafar Fulani, ba mu sauraron labaransu ne kawai
Gwamna Bagudu ya ce Fulani sun fi kowa fuskantar matsalar garkuwa da mutane da kuma satar shanu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A cikin shekarun da suka gabata, Fulani makiyaya ake zargi da kai farmaki tare da sace jama'a, lamarin da ya kawo rikicin kabilanci. Amma sai dai a koda yaushe Fulani suna cigaba da musanta cewa su ke da alhakin wannan hare-haren.

Gwamnan Kebbi ya ce, da yawa daga 'yan Najeriya ba su jin ta bakin Fulani kafin su alakanta su da laifukan, TheCable ta ruwaito.

Ya kara da cewa, da yawa daga cikin Fulani akwai masu natsuwa da son zaman lafiya wandanda neman na kansu kawai suke yi.

"Na samu ganawa da yankunan Fulani da yawa a jiha ta, wanda suka yi min bayanin cewa su aka fara sacewa kuma aka kwace musu shanu," yace.
"Su ne wanda satar jama'a ya fi shafa kuma wannan mugun al'amarin na aukuwa ne daga Fulani da wadanda ba Fulani ba wadanda suka zama 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

“Hakazalika, satar shanu ana yin shi ne ga masu safararsu ko kuma masu shanun. Da yawa daga Fulani su lamarin ke shafa.
“Ba mu sauraron labaran su. Ba mu jin yadda aka yi a bangarensu. Kawai muna tsammanin su ne macutan. Ba kuma dole hakan bane. Da yawansu mutane ne masu son zaman lafiya kuma masu neman na kansu."

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

A wani labari na daban, shugabannin jam'iyya mai mulki ta APC, sun ce kusan makuden kudi da suka kai tiriliyan daya da kadarori shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwato daga mahandama bayan hawansa kujerarsa a APC, Daily Trust ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Alhamis, tsohon sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu, mamba na kwamitin rikon kwarya, Barista Isma'il Ahmed, hadimin shugaban kasa, Tolu Ogunlesi da darakta janar na zauren gwamnonin jam'iyyar, Salihu Lukman, sun ce an samu manyan nasarori.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Kamar yadda takardar ta shaida, gwamnati ta na amfani da kudaden da ta gano ne wurin ayyuka na musamman da kuma sanya hannun jari ko kuma a shigar da su cikin kasafin ko wacce shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng