Zamfara: Dalibi mai shekaru 13 ya sanar da yadda ya kubuta daga miyagu duk da harbinsa da aka yi

Zamfara: Dalibi mai shekaru 13 ya sanar da yadda ya kubuta daga miyagu duk da harbinsa da aka yi

  • Wani Samaila Dahiru, dalibin GDSS Kaya, ya bayar da labarin yadda ‘yan bindigan da suka so kashe malamin sa suka harbe shi
  • Dahiru, mai shekaru 13 ya samu rauni a cinyarsa yayin satar dalibai 73 daga makarantarsu da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara
  • Manema labarai sun tattauna da shi a ranar Asabar bayan an sallame shi daga asibiti, inda ya ce dalibai ‘yan uwan sa ne suka ciccibe shi yayin tafiya cikin daji

Zamfara - Samaila Dahiru, dalibin GDSS Kaya, ya bayyana yadda ‘yan bindigan da suka yi yunkurin halaka malaminsa suka harbe shi amma kuma ya tsira.

Dahiru, mai shekaru 13 ya samu rauni a cinyarsa yayim satar dalibai 73 daga makarantar wacce ta ke karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, TheCable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

Zamfara: Dalibi mai shekaru 13 ya sanar da yadda ya kubuta daga miyagu duk da harbinsa da aka yi
Samaila Dahiru dalibi ne da ya kubuta daga hannun 'yan bindiga duk da harbinsa da aka yi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yayin tattaunawa da TheCable a ranar Asabar bayan an sallame shi daga asibiti, Dahiru ya ce sauran dalibai sun dauke shi a kafadun su yayin tafiya cikin daji.

“Ina aji na hango su, bayan sun shigo makarantar mu sannan suka sace wasu daga cikin mu a kan baburansu. Sun tsawwala mana a kan mu tafi a kasa,” a cewar sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Na tsere da gudu sai suka bi ni. Ina ta kiran Mallam Kabir, malami na, sun yi kokarin harbin sa sai suka harbe ni.
“Daya daga cikin ‘yan ajin mu ya dauke ni a kafadar sa bayan sun harbe ni muka tsere cikin daji. Bayan sun tafi, sai ya mayar da ni gida.”

Aliyu Abubakar, malamin makarantar, ya ce ma’aikatar jin kai ce ta biya kudin maganin Dahiru.

Yayin tsokaci a kan lamarin, malamin ya ce ya na hanyar sa ta zuwa ofishin malamai ya hango ‘yan bindiga suna tafe a babura.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

“Mun fara jarabawa sai muka bai wa yara takardar tsarin jarabawar Mock da JSCE. Na fito daga SS2 ina hanyar zuwa ofishin malamai sai naga baburan su suna tafe,” a cewar Abubakar.
“Muna ta rayuwa cikin tsoro tun bayan aukuwar lamarin. Kun ga jami’an tsaro a garin nan? Haka nan muke, babu wasu jami’an tsaro a garin nan.”

A cewar sa mutanen yankin sun sun roki gwamnatin jihar ta samar da tsaro.

Rikicin cikin gida zai iya tarwatsa mu, Kwankwaso ya ja kunnen shugabannin PDP

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP ya na iya tarwatsa jam'iyyar baki daya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kwankwaso ya ce ba a bukatar irin wannan rikicin a wannan lokacin da jam'iyyar ke fama da rasa mambobin ta.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce tuni ya nisanta kan sa daga dukkan wani rikici kuma kamar yadda ya ce, wadanda ba kwararrun 'yan siyasa ba ne suka hura wutar.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Asali: Legit.ng

Online view pixel