Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai da Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Kasar Guinea

Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai da Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Kasar Guinea

  • Tawagar sojoji na musamman sun tabbatar da rushe gwamnatin shugaba Alpha Conde tare da tsare shi
  • Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da lamarin tare da kiran a gaggauta dawo da gwamnatin demokaradiyya
  • Kakakin ma'aikatar harkokin waje, Esther Sunsuwa, ta bayyana cewa lamarin ya saɓa wa yarjejeniyar ECOWAS

Guinea - Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin da wasu sojoji suka jagoranta a ƙasar Guinea, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamnatin ta yi kira ga mahukuntan ƙasar da su gaggauta yin duk mai yiwuwa a dawo da mulkin demokaradiyya.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi harbe-harbe a fadar shugaban ƙasa kafin daga bisani sojojin su tsare shugaba Alpha Conde.

Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Guinea
Gwamnatin Buhari Ta Yi Allah Wadai da Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Kasar Guinea Hoto: Daily times Nigeria FB fage
Asali: Facebook

Sojojin Guinea na musamman sun yi ikirarin tsare shugaban tare da rushe baki ɗaya wasu hukumomin gwamnatinsa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya aurar da diyarsa Hauwa ga dan Sarkin Azara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojojin sun saɓa yarjejeniyar ECOWAS

A wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya, Esther Sunsuwa, ta fitar, tace juyin mulki ya saba wa dokokin kungiyar kasashen Africa ECOWAS na demokaraɗiyya.

Sanarwar tace:

"Gwamnatin Najeriya ba ta ji daɗin juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Guinea ba yau, kuma a bayyane yake an saɓa wa yarjejeniyar demokaradiyya ta kungiyar kasashen nahiyar Africa ECOWAS."
"Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin kuma ba ta amince da canza gwamnati ta hanyar yiwa doka hawan ƙawara ba."
"Saboda haka muna kira ga masu hannu a wannan lamarin su gaggauta dawo da gwamnatin doka da oda sannan su tabbatar da kare rayukan mutane da dukiyoyinsu."

A wani labarin kuma Ba Maganar Magudi a 2023, NEC Ta Yi Muhimmin Garbawul a Wasu Jihohi

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta yi wasu muhimman canje-canje a wasu jihohin ƙasar nan

INEC ta tura wasu shugabanninta na jihohi (REC) zuwa wasu jihohi na daban yayin da aka maye gurbinsu da wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262