Ba Maganar Magudi a 2023: INEC Ta Yi Muhimmin Garbawul a Wasu Jihohi

Ba Maganar Magudi a 2023: INEC Ta Yi Muhimmin Garbawul a Wasu Jihohi

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta yi wasu muhimman canje-canje a wasu jihohin ƙasar nan
  • INEC ta tura wasu shugabanninta na jihohi (REC) zuwa wasu jihohi na daban yayin da aka maye gurbinsu da wasu
  • Shugaban kwamitin yaɗa labarai, Festus Okoye, shine ya sanar da haka a Abuja ranar Lahadi

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da yin garambawul na canza wasu shugabanninta na jihohi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hukumar ta canza wa wasu shugabanninta na jihohi (RECs) guda biyar daga inda suke aiki zuwa wata jihar, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Festus Okoye, kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, shine ya sanar da haka ranar Lahadi a Abuja, ya kara cewa canjin ya shafi wasu daraktoci huɗu.

Kara karanta wannan

Zaben Kananan Hukumomi: Yan Daba Sun Sace Na'urar Zaɓe Sama da 40 a Kaduna, El-Rufa'i Ya Magantu

Shugaban Hukumar zaɓe ta ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu
Ba Maganar Magudi a 2023: INEC Ta Yi Muhimmin Garbawul a Wasu Jihohi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar Okoye, sabon jadawalin aikin ya maida REC na jihar Osun, Mr. Olusegun Agbaje, zuwa jihar Ogun, yayin da takwaransa na jihar Ogun, Farfesa AbdulGaniy Olayinka Raji, zai maye gurbinsa a Osun.

A jawabinsa yace:

"REC na jihar Bayelsa, Dr. Cyril Omorogbe, zai koma jihar Cross Rivers yayin da na jihar, Emannuel Alex Hart zai maye gurbinsa a Jihar Bayelsa."
"Hakanan an maida shugaban INEC na jihar Zamfara, Dr. Asmau Sani Maikuɗi, zuwa jihar Kaduna."

INEC ta yi gyara a wasu daraktoci

Hukumar ta kuma bayyana cewa daraktan wayar da kan masu kaɗa kuri'a, Mr. Nick Dazang, ya tafi hutun zango bisa haka Mr. Victor Ayodele zai maye gurbinsa.

Hakanan kuma INEC ta sanar da maida, Mista Mikah Thabbal Lakumna zuwa matsayin daraktan sashin shugabanci, daga matsayinsa na daraktan tsaro.

Kara karanta wannan

Tsohon Sakataren Gwamnati Tare da Wasu Mutum 50,000 Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Hukumar tace, Mista Nduh Lebari Samson, zai koma matsayin daraktan tsaro daga ofishin sakataren INEC, yayin da daraktan sashin ayyukan zaɓe, Yakubu Muhammed Duku, zai koma jihar Neja a matsayin sakatare.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Lallasa El-Rufa'i da APC a Zaɓen Kansila Na Gundumar Gwamnan Kaduna

Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a zaɓen kansila na gundunar gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.

Baturen zaɓen gundumar ta Unguwan Sarki, Mohemmed Usman, yace ɗan takarar PDP ya lashe zaɓen kansila a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel