Da duminsa: 'Yan bindiga sun balle gida, sun sace mata da yaran ta mata 2 a Abuja

Da duminsa: 'Yan bindiga sun balle gida, sun sace mata da yaran ta mata 2 a Abuja

  • Masu garkuwa da mutane sun sace wata Oladapo Bukola, mai shekaru 45 da yaranta mata guda biyu a wuraren Kuje dake Abuja
  • An sace su ne bayan kwana biyu da aka sace wani Abdullahi Benda da dan sa Jibrin a wani kauye na Yangoji da ke wuraren Kwali a Abuja
  • Lamarin ya faru ne wuraren karfe 1:04 am na ranar Lahadi kamar yadda wani makwabcin su, Abednego ya tabbatar

Abuja - Masu garkuwa da mutane sun sace wata mata mai suna Mrs Oladapo Bukola mai shekaru 45 da yaran ta 2 a wuraren Pegi da ke Kuje a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa, hakan ta faru bayan kwana 2 da sace wani Abdullahi Benda da yaronsa, Jibrin Abdullahi Benda mai shekaru 23 a kauyen Yangoji da ke Kwali a Abuja.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja

Da duminsa: 'Yan bindiga sun balle gida, sun sace mata da budurwar diyar ta a Abuja
Miyagu sun sake kutsawa wani gida a Abuja, sun sace mata da budurwar diyar ta
Asali: Original

A cikin yaran matar akwai Moyo Oladapo, mai shekaru 17 da wata Glory Oladapo mai shekaru 14.

Mazaunin yankin, Abednego ya ce lamarin ya faru ne da misalin 1:04am na ranar Lahadi.

A cewarsa, masu garkuwa da mutanen sun zo da bindiga kirar AK-47, inda suka kai farmaki har gidan ta da ke Zone A.

A cewar sa, sun tsallake katangar gidan matar ne sannan suka balla kofar, Daily Trust ta wallafa.

Shugaban kungiyar cigaban Pegi (PECDA), Mr Taiwo Aderibigbe ya tabbatar da satar matar da yaran ta yayin tattaunawa da manema labarai.

Shugaban PECDA ya koka a kan yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin kuma ya bukaci taimakon jami’an tsaro.

“Lamarin ya na da ban tsoro, yanzu Pegi da Kuje sun zama wurin da masu garkuwa da mutane suke kai farmaki kuma jami’an tsaro ba sa wani kokari,” a cewar sa.

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun koma ruwa, sun shiga hannun 'yan sanda a Katsina

Daily Trust ta ruwaito yadda mijin matar, Fasto Gabriel Oladapo, ya yi tafiya lokacin da masu garkuwa da mutanen suka kai farmakin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’ar ‘yan sandan Abuja, ASP Daniel Y Ndiparya, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace suna iyakar kokarin ganin sun ceto su.

“Yan sanda su na ta kokarin ganin an ceto su,” a cewar sa.

Allah ne ya haɗa mu: Kwankwaso ya magantu kan haɗuwar shi da Ganduje

A wani labari na daban, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bada labarin yadda suka hadu da wanda ya gaje shi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, manyan 'yan siyasan biyu sun hadu a filin sauka da tashin jiragen sama da ke Abuja kuma sun hau jirgi daya zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun fasa coci, sun yi awon gaba da masu ibada

Su biyun sun yi aiki tare a shekaru masu yawa da suka gabata, sun kuma raba jiha tun bayan da Ganduje ya gaji kujerar Kwankwaso a shekarar 2015. A yayin da Kwankwaso ya jagoranci jihar Kano, Ganduje ne mataimakinsa tsakanin 1999 zuwa 2003.

Asali: Legit.ng

Online view pixel