Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja

  • Yan bindiga sun sace wani mutum da dansa a kauyen Yangoji a birnin tarayya Abuja
  • Wani makwabcin mutumin ya bada labarin yadda yan bindigan suka sace mutumin da dansa
  • Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta san da afkuwar lamarin kuma tana kokarin ceto wadanda aka sace

FCT, Abuja - An sace wani mahaifi, Abdullahi Benda, da dansa mai shekaru 23, Jibrin Abdullahi Benda a gidansu da ke kauyen Yangoji a karamar hukumar Kwali ta Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja
Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Gida Sun Sace Mahaifi Da Ɗansa a Abuja
Asali: Original

Makwabin wanda aka sace ya magantu

Daily Trust ta ruwaito cewa wani makwabcinsu da ya ce sunsa Zakari ya ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce masu garkuwar da suka tsaya a wurare daban-daban sun haura katanga ne sun shiga gidan wanda abin ya faru da shi.

Ya ce:

"Daya daga cikin masu garkuwar ya tsaya kusa da taga ta yana ta ihu, domin katanga ne kawai ke tsakaninmu da gidan wanda aka sace.

"Sauran yan tawagar sun haura katanga sun shiga cikin gidan."

Ya ce masu garkuwar sun bude kofar gidan da karfi da yaji sannan suka shiga dakinsa suka sace mutumin da bindiga tare da daya daga cikin yayansa.

Ya kara da cewa:

"Sun yi yunkurin tafiya da matar mutumin amma daga baya suka kyalle ta bayan sun lura tana shayar da jinjiri."

Abinda 'yan sanda suka ce game da lamarin?

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan birnin tarayya Abuja, ASP Daniel Y. Ndiparya ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa rundunar tana kokarin ganin an ceto wadanda aka sace din da ransu.

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

Ya ce:

"Muna da masaniya kan abin da ya faru, rundunar na kokarin ganin ta ceto wadanda aka sace din."

'Yan Bindiga Sun Sace Sakataren NASIEC a Nasarawa

A wani labarin daban, Ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mohammed Okpu, sakataren Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Jihar Nasarawa, The Cable ta ruwaito.

Hakan na cikin wata sanarwar ne da mai magana da yawun yan sandan jihar Nasarawa, Rahman Nansel, ya fitar a ranar Laraba a Lafia.

The Cable ta ruwaito cewa Nansel ya ce kimanin yan bindiga biyar ne suka kutsa gidan sakataren na NASIEC a ƙauyen Bakin Rijiya da ke hanyar Lafia-Shendam misalin ƙarfe 11.45 na daren Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164