Da Ɗumi-Ɗumi: An Ɗage Zaɓukan Ƙananan Hukumomi 4 a Jihar Kaduna

Da Ɗumi-Ɗumi: An Ɗage Zaɓukan Ƙananan Hukumomi 4 a Jihar Kaduna

  • Hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kaduna, KADSIECOM, ta dage zabukan da aka shirya yi a ranar asabar a kananan hukumomi 4 a jihar
  • Hukumar ta KADSIECOM ta bakin shugabanta Dr Saratu Dikko Audu ta ce an dage zabukan ne saboda rahoto da ya nuna za a iya samun matsalar tsaro
  • KADSIECOM ta sauya ranar yin zabukan a kananan hukumomin Zangon Kataf, Birnin Gwari, Chikun da Kajuru zuwa ranar Asabar 25 ga watan Satumba

Jihar Kaduna - Hukumar zabe mai zaman kanta na Jihar Kaduna, KADSIECOM, ta dage zabukan kananan hukumomi da aka shirya yi a ranar Asabar a kananan hukumomi hudu a jihar saboda rashin tsaro, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Kaduna ta haramta safarar dabbobi daga wasu jihohi

Da Ɗumi-Ɗumi: An Ɗage Zaɓukanan Ƙananan Hukumomi 4 a Jihar Kaduna
Masu yi wa kasa hidima yayin gudanar da zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar, a ranar Juma'a, ta ce an dage zabukan ne biyo bayan samun rahoton tsaro wadda ya nuna ba zai yi wu a gudanar da zabukan ba cikin lumana a kananan hukumomin Kajuru, Birnin Gwari, Chikun da Zangon Kataf.

Abin da shugaban KADSIECOM ta ce?

Rahoton na Daily Trust ya ce Shugaban hukumar, Dr Saratu Binta Dikko-Audu ya ce dagewar ya zama dole ne domin kare rayyuka da dukiyoyin mutane harda ma'aikatan zaben da kayan aiki.

Ta ce:

"Yanzu za a gudanar da zabukan a wadannan kananan hukumomin a ranar Asabar 25 ga watan Satumban 2021.
"Mun yi imanin cewa za a iya tura dukkan jami'an tsaro zuwa wadannan kananan hukumomin domin zaben a ranar da aka zaba domin kare afkuwar rikici da kiyayye rasa rayuka da dukiyoyi."

Ta yi kira da 'yan siyasa da mazauna jihar da su cigaba da zama da juna lafiya ta hanyar za a yi zaben cikin lumana.

Kara karanta wannan

Hukumar yan sanda ta bayyana adadin daliban da aka sace a jihar Zamfara yau

Shugaban na KADSIECOM ta ce hukumar za ta gudanar da zabe sahihi kuma za ta yi wa kowa adalci.

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel