‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi

‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi

  • Hukumar 'yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa wasu mahara sun halaka mutum guda tare da jikkata wani daya a yankin Burshin Fulani da ke jihar
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil ne ya tabbatar da hakan
  • Ya kuma bayyana cewa sun kai farmakin ne da sanyin safiyar ranar Asabar

Rundunar ‘yan sanda a Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutum daya da raunata wani a wani hari da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai a yankin Burshin Fulani da ke cikin garin Bauchi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan bindigar sun afka wa al’ummar ne da sanyin safiyar ranar Asabar inda suka far wa mazauna yankin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan sanda sun yi nasarar kasha Shugaban IPOB/ESN a kudu maso gabas

‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi
‘Yan bindiga sun halaka mutum daya tare da jikkata wani a jihar Bauchi Hoto: The eagleonline
Asali: UGC

Wakil ya ce 'yan bindigar da ba a iya tantance adadinsu ba sun kai hari kan al'ummar, inda suka kashe mutum daya tare da jikkata wani mutum guda.

Ya ce:

“Wasu‘ yan bindiga sun kai hari kauyen Burshin Fulani inda suka kashe mutum daya, Abubakar Muhammad, babban ma’aikacin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Bauchi.
“An harbe shi a wuya kuma nan take ya mutu. 'Yan sandan da suka garzaya wurin da lamarin ya faru sun kwashe wanda abin ya rutsa da shi zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), Bauchi, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
“Rundunarmu ta sintiri da ke kofar kwalejin ta ji karar harbe-harben bindiga daga wajen da misalin karfe 4: 00 na asuba sannan cikin gaggawa ta isa yankin, da ganin hasken motar sintiri sai ‘yan bindigar suka gudu.

Kara karanta wannan

Bauchi: 'Yan sanda sun yi ram da mutum 352 da ake zargi da garkuwa da mutane

“Marigayin ya fito don ceto yaransa da ke kokawa da wasu mutane a bakin kofa, nan take ya fito, suka harbe shi.”

Wakil ya kuma ruwaito Kwamishinan ‘yan sanda, Sylvester Alabi, yana umartar ‘yan sandan da su bi ‘yan bindigar sannan su gurfanar da su a gaban kuliya, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Yan bindiga sun hallaka mutum 22 don an kashe musu 'yan uwa a Neja

A wani labarin, Yan bindiga a daren Juma'a su kai mumunan hari garin Magami dake karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja inda suka hallaka mutum akalla 20 lokaci guda.

Sakamakon wannan hari, mutan garin sun gudu daga muhallansu zuwa wasu garuruwa.

Mazauna garin sun ce wannan ramuwar gayya ce yan bindiga suka kai don an kashe musu yan'uwa yan bindiga a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel