An yi cece-kuce yayin da shugabar karamar hukuma ta rabawa manoma tallafin fatanya, adda da doya guda

An yi cece-kuce yayin da shugabar karamar hukuma ta rabawa manoma tallafin fatanya, adda da doya guda

  • Shugabar karamar hukumar Obanliku ta jihar Kuros Riba, Evangelist Margaret Inde, ta sa mutane suna cece kuce a soshiyal midiya
  • Inde ta sha caccaka saboda ta raba wa manoma fatanya, adda da doya guda ɗaya a matsayin tallafi
  • Shugabar ta raba waɗannan abubuwan ne yayin bikin fitowar sabon doya wanda aka yi a ranar Juma'a, 27 ga Agusta
  • Mutane da yawa da suka bayyana ra’ayoyin su game da ci gaban sun yi mamakin dalilin da yasa manoma ke jin daɗin karɓar irin waɗannan abubuwa a matsayin tallafi

Kuros Riba - Shugabar karamar hukumar Obanliku na Kuros Riba, Evangelist Margaret Inde, ta baiwa manoma tallafi da fatanya, adda da doya daya.

A cewar Sahara Reporters, manoman sun karbi kayayyakin ne a lokacin taro don murnar cika shekaru 30 da kafa karamar hukumar tare da bikin fitowar sabon doya da aka yi a ranar Juma’a, 27 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

An yi cece-kuce yayin da shugabar karamar hukuma ta rabawa manoma tallafin fatanya, adda da doya guda
An yi cece-kuce yayin da shugabar karamar hukuma ta rabawa manoma tallafin fatanya, adda da doya guda Hoto: Adins Maryo
Asali: Facebook

'Yan Najeriya a shafukan sada zumunta ba su ji dadin wannan karamci na shugabar ba kuma da yawa daga cikinsu sun bayyana ra'ayinsu kan ci gaban.

Da take wallafa hotunan tallafin a shafinta na Facebook, Adins Maryo ta rubuta:

"Evangelist Margaret Inde, babbar Shugabar karamar hukumar Obanliku a jihar Cross Rivers ta tallafawa matasa da doya, adda da fatanya. Irin wannan shugaba mai aikin al’ajabi."

'Yan Najeriya sun maida martani

Ude Gabriel ya ce:

"Chai ... kuma mutanen ma sun jeru don karbar kayan, Abin tausayi ne. Tallafi na gaba da za a basu zai kasance man ja da itace."

Frank Nnamdi yayi sharhi:

"wayyo Allah .... yaya aka yi na kasance a kasar nan ??"

Justus Onyemachi ya rubuta:

"Saboda wani dalili?"

Red Ivy Osarumwense ya ce:

Kara karanta wannan

Benue: Masu ruwa da tsaki na APC sun nemi Buhari ya ayyana dokar ta baci

"Don su yi me da su."

David Ola Peju yayi sharhi:

"Da gaske kake?"

Akpabuo Greg yayi sharhi:

"Maimakon matasa su yi mata dukan tsiya su nemi tallafi mai kyau suna gaisawa da ita. Posterity zai yanke mata hukunci. Shin idan mutum ya kasance talaka sai ya gasa tunani? Yan siyasa ku ji tsoron Allah fa!”

A wani labari, gwamnatin tarayya ta fara biyan tallafin N20,000 ga mutane 74,000 a jihar Kogi, waɗanda aka tantance karkashin shirin CCT, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnati ta kirkiro shirin CCT (Conditional Cash Transfaer) ne domin bada tallafin N5,000 ga magidanta masu karamin karfi karkashin tsarin NSIP a ma'aikatar jin kai da walwala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel