Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

Hotunan doya da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta raba wa manoma a matsayin tallafi ya janyo maganganu

  • Margaret Inde, shugaban karamar hukumar Obanliku a jihar Cross Rivers ta raba wa mutane doya da fatanya da adda daya
  • Shugaban karamar hukumar ta bada wannan tallafin ne ga matasa a yayin da ake bikin cika shekaru 30 da kirkirar karamar hukumar
  • Hotunan bikin rabon wannan kayan tallafin ya janyo hankulan mutane da dama inda suka rika bayyana ra'ayoyinsu

Shugaban karamar hukumar Obanliku a jihar Cross Rivers, Evangelist Margaret Inde, ta bawa sabbin manoma tallafin doya da fatanya da adda, daya-daya a matsayin tallafi, rahoton LIB.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Inde ta mika kayan tallafin ne yayin bikin cika shekaru 30 da kirkirar karamar hukumar da kuma bikin fitowar sabuwar doya ta bana da aka yi a ranar Juma'a 27 ga watan Agusta.

Hotunan doya ɗaya kacal da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta rabawa manoma matsayin tallafi a Cross Rivers
Hotunan manoma da aka raba wa fatanya da doya da adda a Cross Rivers. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Lalong ya rufe majalisar jihar Filato don hana tsige shi? Gwamnan ya bayyana gaskiyar lamari

A wasu hotuna da suka bazu a dandalin sada zumunta, an gano shugaban karamar hukumar tana bawa mutanen yankin ta tallafin doya daya, da fatanya da adda.

Wannan tallafin da ta yi ya janyo cece-kuce sosai tsakanin ma'abota amfani da shafukan dandalin sada zumunta.

Hotunan doya ɗaya kacal da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta rabawa manoma matsayin tallafi a Cross Rivers
Hotunan manoma da aka raba wa da doya da fatanya da adda a Cross Rivers. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Hotunan doya ɗaya kacal da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta rabawa manoma matsayin tallafi a Cross Rivers
Hotunan manoma da aka bawa tallafi a Cross Rivers. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Hotunan doya ɗaya kacal da fatanya da shugaban ƙaramar hukuma ta rabawa manoma matsayin tallafi a Cross Rivers
Hotunan manoma da aka raba wa fatanya da doya a Cross Rivers. Hoto: LIB
Asali: Facebook

A jawabin da ta yi wurin bukukuwan da aka yi a Sankwala, hedkwatar Obanliku, shugaban karamar hukumar ta jinjinawa al'ummarta, ta kuma taya su murnar cika shekaru 30 da kafuwa sannan ta yi kira ga cewa a zauna lafiya.

Wasu daga cikin abubuwan da ma'abota amfani da shafukan sada zumunta ke cewa

Emmanuel Owoya Ekpo ya ce:

"Wannan ai bautar da mutanen ki ne da kuma kunyata garin ku."

Stanley Chiemeka Ohanehi ya ce:

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar kwastam sun cafke wata mota dauke da bindiga da harsasai

"Shin wannan mutanen nakasasu ne? ... Me yasa za su amince da irin wannan cin mutuncin. Allah ya kawo mana sauki."

Inegbedion Joseph ya ce:

"Kaico! Ina zubar da hawaye saboda kasa ta Nigeria"

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Asali: Legit.ng

Online view pixel