Yanzu Yanzu: An yi gagarumin sauyi a majalisar Shugaba Buhari, an sallami ministoci 2 daga arewa
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba ya sauke ministoci biyu daga mukamansu
- Ministocin sune na ma’aikatar gona, Mohammed Sabo Nanono, da takwaransa na ma’aikatar wutar lantarki, Saleh Mamman
- Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin labarai, Femi Adesina, ne ya sanar da wannan
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a majalisar ministocinsa, inda ya sanar da sallamar wasu ministoci biyu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ministocin da aka sauke sune na aikin gona, Mohammed Sabo Nanono da takwaransa na ma’aikatar wutar lantarki, Mamman Saleh.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 1 ga watan Satumba, jaridar Tribune ta ruwaito.
Ya ce an sauyawa karamin ministan muhalli, Mohammed Abubakar, waje zuwa ma'aikatar aikin gona yayin da karamin ministan ayyuka, Mista Abubakar Aliyu, zai zama ministan wutar lantarki.
Ya ce za a cike guraben da babu kowa kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Kashe-kashen Benue: An nemi DSS ta binciki Ministan Buhari
A gefe guda, mun kawo cewa alamu sun nuna cewa abubuwa sun juya kan ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci, Sanata George Akume, kan kiran da ya yi wa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na su binciki gwamna Samuel Ortom.
Dangane da abin da Akume ya gabatar, Jam’iyyar PDP ta nemi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta bincike shi kan zargin hannu a kisan Benue, jaridar This Day ta rahoto.
A cikin wata sanarwa ta hannun sakataren yada labaran ta na kasa, Kola Ologbondiyan, PDP ta ce rokon da ta yi wa DSS ya dogara ne kan tunanin Akume game da kashe-kashen da ke faruwa a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng