Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

  • Majalisar dokokin jihar Filato ta yi Allah wadai da kashe-kashen da ke faruwa a garuruwa daban-daban a Jos
  • Wasu mazauna jihar ba su ji dadin yadda gwamna Simon Lalong ya tafiyar da lamarin ba
  • 'Yan majalisa a Filato sun yi kira ga Lalong da ya fito da kwararan matakai kan yadda za a dakatar da kalubalen tsaro a jihar

Rahotannin da ke fitowa sun nuna cewa ‘yan majalisar dokokin Filato na fuskantar matsin lamba na tsige gwamna Simon Lalong kan karuwar hare -hare a jihar.

An dora alhakin rikicin jihar kan karo tsakanin 'yan asalin yankin da Fulani mazauna yankin.

Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya
Gwamna Simon Lalong na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya Hoto: Governor Simon Bako Lalong
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa mazauna jihar da suke ganin Gwamna Lalong yana da ra’ayin Fulani ne ke neman a dauki mataki akan gwamnan.

Rahoton ya bayyana cewa wasu daga cikin 'yan majalisar sun tabbatar da cewa suna fuskantar matsin lamba daga 'yan mazabarsu da suka zarge su da hadewa da gwamnan don yin watsi da su cikin rashin tsaro.

Wani dan majalisar da baya son a ambaci sunansa ya bayyana cewa har yanzu majalisar bata yanke shawara kan ko za a fara sharin tsige gwamnan ba ko a’a.

Ya ce majalisar za ta yanke hukunci idan gwamnan ya gaza magance matsalolin tsaro da ke damun jihar cikin makwanni biyu.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Philip Dasun, shugaban kwamitin majalisar kan bayanai ya shaidawa manema labarai a Jos cewa yan majalisan sun himmatu wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar.

Ya ce:

"A matsayin mu na majalisa da ke dauke da mutane a zucciyarmu, muna kira ga 'yan Filato da su kasance masu dogaro da mu.
“Mun bai wa gwamnan makonni biyu ya dauki mataki kan kudurorin da majalisar ta gabatar kan harkokin tsaro da yadda za a maido da zaman lafiya.
"Muna kira ga Gov. Simon Bako Lalong ya fito da wata sanarwa da za ta kare mu a matsayin mu na al'umma da kuma dawo da sabon sadaukar da kai ga aikin Filato.”

Kashe-kashe: Ku kare kanku, majalisar Filato ta bukaci mazauna

A baya mun kawo cewa majalisar dokokin jihar Filato ta nemi mazauna yankin da su kare kansu. Jihar ta fada cikin rikici a 'yan makonni biyu da suka gabata.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Dasun Philip Peter, ya ce tsarin tsaro na yau da kullun ba zai iya ba da tabbacin tsaro ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel