An shiga halin fargaba yayin da PDP ta rasa manyan jiga-jiganta 4 cikin makonni 6
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Legas tana cikin alhini kan mutuwar manyan jiga-jiganta
- Adegbola Dominic, shugaban jam'iyyar, ya mutu a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, sakamakon cutar COVID-19
- Kwanaki kafin rasuwarsa, jam'iyyar ta rasa sakatarenta, Prince Muiz Shodipe-Dosunmu, bayan gajeriyar rashin lafiya
Lagos - Mutuwar shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Adegbola Dominic, sakataren jam'iyyar, Prince Muiz Shodipe-Dosunmu, da wasu manyan jiga-jigai biyu sun haddasa rikicin shugabanci a tsakanin mambobin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an samu rudani a cikin jam’iyyar kan wanene sahihin shugaba yayin da ake fafutukar neman kujerar a tsakanin Deji Doherty da Dominic har zuwa rasuwar marigayin.

Asali: UGC
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa shugaban na PDP a jihar Legas ya rasu da yammacin ranar Laraba, 25 ga watan Agusta.
Legit.ng ta tattaro cewa mutuwar Dominic ya kasance kafin na Prince Shodipe-Dosunmu kamar yadda aka ce shugabannin sun mutu ne sakamakon cutar korona.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar rahoton, wani jigon jam'iyyar a Agege, Injiniya Auwal Tahir-Maude, ya ce mambobi da yawa sun shiga rudani game da shugabancin jam'iyyar.
Sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka rasu kwanan nan sune; mataimakin shugaban jam’iyyar; Legas ta yamma, Alhaji Monsuru Ajagbe da shugabar mata, Yeye Shola Oladehinbo.
Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya ce bai san da wannan ci gaban ba.
A wani labari na daban, mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Bamaina da ke karamar hukumar Birnin Kudu ta Jigawa sun bukaci tsohon gwamnan jihar, Sule Lamido da ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.
‘Ya’yan babbar jam’iyyar adawar kasar sun bayyana haka ne a wani karamin taro da aka yi a garin Lamido a ranar Talata, 31 ga watan Agusta, jaridar PM News ta ruwaito.
Asali: Legit.ng