Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya

Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya

  • Rikicin shugabancin jam'iyyar PDP ya dau sabon salo
  • Kwana daya bayan nada sabon shugaba, Uche Secondus ya ce har yanzu shine shugaba
  • Ya dira hedkwatar don shiga ofishinsa bayan an baiwa wani

Abuja - Shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party PDP, Uche Secondus, da dimbin magoya bayansa sun dira hedkwatar jam'iyyar. Wadata Plaza. dake birnin tarayya Abuja ranar Juma'a.

Secondus ya dira ofishinsa ne misalin karfe 9:15 na safe gabanin zaman kwamitin gudanarwan jam'iyyar da aka shirya karfe 10 na safe, rahoton Punch.

Ya koma ofishinsa ne yau bisa umurnin kotun jihar Kebbi da ta mayar da shi kan kujerarsa.

A makon da ya gabata, babbar kotun jihar Rivers ta umurci Secondus ya daina kiran kansa shugaban jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Maida Uche Secondus Mukaminsa Na Shugaban Jam'iyyar PDP

Bisa hakan majalisar dattawan jam'iyyar da kwamitin gudanarwa suna amince da mataimakinsa, Yemi Akinwunmi, a matsayin mukaddashin shugaba.

Amma a ranar Alhamis, wata babbar kotun jihar Kebbi dake zamanta a Birnin Kebbi ta yi watsi da umurnin kotun jihar Rivers.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya
Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya
Asali: Facebook

Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya
Rikicin PDP ta dawo danya: Uche Secondus ya dira hedkwatar jam'iyyar da dimbin masoya
Asali: Facebook

PDP ta Nada Sabon Shugaba Na Kasa

A jiya mun kawo muku cewa bayan kwanaki biyu ana dambarwa kan shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, an nada mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa (kudu), Yemi Akinwonmi a matsayin mukadashin shugaba.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ne ya sanar da hakan bayan taron sirri da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta yi a ranar Alhamis a Abuja.

Rikicin PDP ya kare, Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya rikicin dake cikin jam'iyyar PDP yazo karshe, kuma zasu lashe zabe a 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Sanata Stella Oduah ta sauya sheka daga PDP zuwa APC

"Na yi imanin PDP za ta cika burikan mutanen Najeriya saboda sun san mu fiye da kowace jam'iyya."
"Masu farin cikin cewa an samu baraka cikin PDP, yanzu ban sani ko zasu koma ba saboda an dinke barakar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng